APC a Katsina na yunkurin hukunta Ministan Buhari da dan uwansa

APC a Katsina na yunkurin hukunta Ministan Buhari da dan uwansa

Ministan sufurin jiragen sama, Santa Hadi Sirika; Manajan Darakta na wani babban bankin zamani, Ahmed Musa Dangiwa; da Manajan Darakta na hukumar jiragen ruwa na Najeriya, Hadiza Bala Usman, na iya fuskantar hukunci daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Katsina kan zargin cin dunduniyar jam'iyyar, inciken jarida Thisday ya bayyana.

Sauran wadanda ka iya fuskanta hukunci daga jam'iyyar mai mulki sun hada da Sama’ila Isa Funtua, Mamman Daura, Sani Zangon Daura Musa Haro (dan uwan Buhari) da Sabiu Tunde.

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa an zargi dukkaninsu da mara wa dan takaar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Sanata Yakubu Lado Danmaka baya, domin dakile nasarar Gwamna Aminu Bello Masari a kotun daukaka kara.

Jam'iyyar ta kuma gargadi wadanda ta bayyana a matsayin maasa da'a da su janye daga sanya baki a siyasar jihar Katsina, inda tace lallai zata yi masu ritaya daga siyasa idan suka jin gargadinta.

KU KARANTA KUMA: Lalata da dalibai domin basu maki a jarrabawa: An kori babban lakcara a jami'ar Najeriya

Gwamnan yayi korafin cewa tun daga mulkinsa na farko yana ta fama da al’amuran fa suka shafi kotu, al’amuran da ya bayyana a matsayin ayyukan makiyansa dake cikin gwamnatin da APC ke jagoranta a jihar.

Duk da haka, ya gargadi magoya bayan APC a jihar dasu guji jawaban tunzura wadanda ka iya haddasa rashin kwanciyar hankali a jam’iyyar, inda ya kara da cewa babu cigaba mai amfani da za samu a yanayin da ke cike da tashin hankali.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel