Hira ta musamman tare da Janar Kunle Togun game da mutuwar Dele Giwa

Hira ta musamman tare da Janar Kunle Togun game da mutuwar Dele Giwa

Tsohon shuganan hukumar DMI wanda kuma ya taba rike mataimakin shugaban hukumar DSS a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida watau Ajibola Kunle Togun yayi magana a kan Dele Giwa.

Janar Ajibola Kunle Togun ya yi maganar ne a lokacin da ya yi wata hira da ya yi da Ridwan Kolawole na Jairdar Legit.ng a Abuja. Kunle Togun ya tabo maganar da ba kasafai aka saba yin ta ba.

Tsohon shugaban na SSS a lokacin ya bayyana cewa a kan Dele Giwa ne aka fara amfani da bam din takarda wajen kashe mutum a Najeriya. Giwa ya na aiki ne da Jaridar NewsWatch a wancan lokaci.

“Segun Adeniya ta taba takura mani cewa zai yi hira da ni a lokacin ya na aiki da Jaridar Concord. Mu na fara magana ya tado da batun Dele Guwa. Na ce masa shi ba za ka iya kawo kananan zance ba.?”

“Koyode Soyinka ya bada labarin abin da duk ya auku, ya ce ya zauna ga shi-ga Dele Gia kuma su ne su ka kawo masa ambular irin wanda aka saba bada sakon littatafai a ciki. Yace shi ya kai wa Dele Giwa.”

KU KARANTA: Wasu manya a Gwamnatin Buhari su na neman hanyar ganin bayan Osinbajo

A cewar Soyinka, kai wa Giwa ambular ke da wuya, sai ta yi bindiga tun kafin ya bude. Ya yi ikirarin ya jikkata a lokacin da ambular ta tashi. Janar AK Togun ya nuna akwai alamar tambaya a nan.

Janar Togun ya ke cewa karafunan dakin duk sun rugurguje, na’urar rubutu ta karye, tagogin dakin dakin da na’urar AC duk sun bare amma ko kwarzane babu a jikin Kayode Soyinka. Wannan zai yiwu?

Togun ya kara da cewa: “A lokacin da wata Baiwar Allah ta nemi ta shigo dakin sai ta iske an garkame shi, ta sa hannu ta fasa kofar ta bude. Abin a sake tambaya a nan shi ne wa ya rufe dakin kenan?

Tsohon Sojan ya kuma lura raunin da Giwa ya samu ba na bam bane. Kayan barcinsa ne ya narke a jikin kirjinsa. Yace mutum biyu su ka sanya wannan kayan barcin da shi kansa Soyinka ya saya masu.

Babban Jami’in tsaron wanda yanzu ya yi ritaya yace ba zai bada cikakken labarin abin da ya faru kan mutuwar Dele Giwa ba, wanda yace har littafi ya rubuta kwana biyar rak da rasuwar ‘dan jaridar.

AK Togun yace hukumar DSS ne ya kamata su binciki lamarin amma da aka fara zarginsa da hannu kan mutuwar, sai ‘yan sanda su ka yi binciken. “Mun fada masu abubuwan da ya kamata su duba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel