Ka bai wa malaman Najeriya kwangilar addu’a idan kana son tsaron kasar – Shehu Sani ga Zulum

Ka bai wa malaman Najeriya kwangilar addu’a idan kana son tsaron kasar – Shehu Sani ga Zulum

- Tsohon sanatan arewa, Shehu Sani, yayi kira ga a bai wa malaman Najeriya kwangilar addu'a amma ba wai takwarorinsu na kasa Saudiyya ba

- Sani ya bayyana cewa kamata yayi yan Najriya su tuntubi fastoci a kasar domin addu'a tunda hakan ne sabon dabara na tabbatar da tsaron kasar

- Tsohon sanatan ya bayyana cewa manufa akan kayayyakin kasa kada ya tsaya kan shinkafa yar gida kawai

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, yayi kira ga yan Najeriya da su ba ,malaman kasa kwangilar addu'a tunda a yanzu addu'a cewa sabuwa hanyar tsaron kasa.

Shehu Sani ya bayyana cewa babu bukatar yan Najeriya su tafi neman malaman kasar Saudiyya mai makon haka a bai wa yan kasa kwangilar wannan aiki duk a cikin manufar dogaro da kayayyakin gida.

Tsohon sanatan a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa kada dogaro da kayayyaki yan gida ya tsaya kan shinkafar Najeriya kawai.

Furucin nasa martani ne ga kira da Gwamna Babagana Zulum yayi a Borno a ranar Juma'a, 4 ga watan Oktoba zuwa ga malamai 30 daga wasu jihohin arewa akan su taimaka a sha karfin yan ta'addan Boko Haram ta hanyar yin addu'o'i.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram sun far ma fadar sarki a wani sabon hari da suka kai Yobe

A baya mun ji cewa Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya bai wa wasu malamai kimanin 30 mazauna birnin Makkah na kasar Saudiya, kwangilar gudanar da addu'o'i da kuma dawafi domin rokon Mai Duka ya magance musibar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau, ya ce gwamnatin Borno ta bai wa wadannan malamai 30 mazauna birnin Makkah kwangilar gudanar da addu'o'i wajen rokon 'Buwayi Gagara Misali' da ya wanzar da aminci a jihar da kuma kasa baki daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel