Rudani: Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta dare gida biyu

Rudani: Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta dare gida biyu

Ma'aikatar kwadago da aiyuka ta tabbatar da karbar takardar neman yin rijista daga wa wata kungiyar malaman jami'o'i mai lakabin CONUA wacce aka kirkira daga cikin kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU).

A wata hira da shi ta wayar tarho, ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, ya tabbatar da cewa kungiyar malaman dake koyar wa a jami'o'i (CONUA) ta nemi a yi mata rijista a matsayain sabuwar kungiyar malamai a jami'o'i.

Ya ce takardar neman rijistar da sabuwar kungiyar ta aiko zata bi ta hannun wani kwamiti da zai duba dacewar yin hakan bisa tsarin dokokin kungiyoyin ma'aikata.

"Ba a yi musu rijista ba har yanzu, amma takardarsu ta neman rijista tana ma'aikatar kwadago. Ba mu fara duba bukatarsu ba ya zuwa yanzu.

"Har yanzu muna duban takardar bukatar da suka aiko. Na kafa kwamiti da zai duba bukatarsu domin ya bamu shawarar abinda ya kamata mu yi.

"Sun fara kawo takarda ta farko tun kafin a sauke mu a zango na farko, sun kara aiko da ita a watan Afrilu," a cewarsa.

Da aka tambayi ministan ko aiyukan kungiyar da na ASUU ba zasu ke cin karo ba, sai ya ce kwamitin da aka kafa zai duba hakan.

Shugaban kungiyar CONUA na kasa, Niyi Ismaheel, ya shaidawa manema labarai a Abuja, cewa babban dalilin kafa kungiyarsu shine domin su sabunta hanyoyin yadda ake gudanar da kungiya da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jami'o'in Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel