‘Dan wasa Ronaldo ya fara harin ajiye wasan kwallon kafa nan da shekara 1 ko 2

‘Dan wasa Ronaldo ya fara harin ajiye wasan kwallon kafa nan da shekara 1 ko 2

Fitaccen ‘Dan kwallon kasar Portugal Cristiano Ronaldo ya fara hangen lokacin da zai ajiye takalman wasansa ya yi ban kwana gaba daya daga buga kwallon kafa bayan shekara da shekaru.

Babban ‘Dan wasan na Duniya wanda har gobe yake tashe a shekara 34 ya fara nuna cewa ya na iya yin ritaya nan da shekara guda ko biyu. Wannan ya ba akasarin masu kallon kwallo mamaki.

Tsohon ‘dan wasan Real Madrid din ya na da kwangila da Juventus har zuwa 2022, bayan ya koma kungiyar a bara. Sai dai tun kafin tafiya ta yi nisa, Ronaldo ya fara hangen yin ritaya.

Cristiano Ronaldo ya shafe kusan shekaru goma kenan tauraruwarsa ta na haskawa. Likitoci da sauran Masana kwallo su na ganin cewa ‘dan wasan ya na da lafiyar buga kwallo har nan gaba.

KU KARANTA: Ronaldo ya sharara kuka bayan ya tuna da Tsohonsa

“Ina son kwallon kafa,” Ronaldo ya ke fadawa SportBible. “Ina sha’awar ganin na burge ‘yan kwallo da duk masu kaunar Ronaldo. Shekaru ba shi bane abin dubawa a yanzu. Zuciyarce kurum.”

Ronaldo ya cigaba: “Shekaru biyar din nan da su ka wuce, na fara jin dadin hararo rayuwa ta a wajen kwallon kafa. Saboda haka wa ya sani ko nan da shekara guda ko kuma shekaru biyu?”

Gwarzon ‘dan wasan wanda ya lashe kyautar ‘dan kwallon Duniya sau 5 a tarihi ya bude wani gidan turare da kamfanonin tufafi da otel. Bayan haka kuma ya na da asibitin gyaran gashi.

Duk a cikin shirin ritaya, kamfanin Nike ta ba shi kwangilar har abada inda zai samu kudi Dala biliyan guda. An yi wannan yarjejeniya da ba a taba yi a Duniyar kwallo ba ne da Ronaldo a 2016.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng