Fintiri barazana ne ga rayuwar Jam’iyyar PDP a Adamawa – Sanata Abbo

Fintiri barazana ne ga rayuwar Jam’iyyar PDP a Adamawa – Sanata Abbo

Mun samu labari a yau Laraba 2 ga Watan Oktoba na 2019 cewa Sanata Ishaku Elisha Abbo ya zargi gwamna Ahmadu Fintiri da yin wani irin salon mulki na kama-karya a jihar Adamawa.

Sanatan ya na zargin gwamnansa da su ke jam’iyya daya da nuna karfa-karfa a cikin tafiyar jam’iyyar. Ishaku Elisha Abbo ya ce gwamnan ya na kakaba ‘yan takararsa a zaben da za ayi.

Zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar Adamawa ne ya jawowa Mai girma gwamna Ahmadu Fintiri suka wajen Sanatansa inda ‘dan majalisar yace gwamnan ya kama hanyar ruguza PDP.

Elisha Abbo ya jefi gwamnan na Adamawa da wannan zargi ne a Ranar Talata inda ya ce gwamna ya na kokarin tursasawa kananan hukumomin jihar wadanda yake so a matsayin ‘yan takara.

“A dalilin karanta da kama-karyar Fintiri a kan mulki da rikon jam’iyya, PDP ta zarce gargara a Adamawa, yanzu har ta koma kan na’urar da ke ceto ran da ke hannun Ubangiji. Inji Abbo.

KU KARANTA: Atiku ya shiga ya fita domin shawo kan rikicin PDP a Kogi

“’Manyan ‘yan siyasar da aka hana takara a jam’iyya da Iyayen gidansu da Mabiyansu za su jira zuwa lokacin da ya dace domin su yi wa Fintiri illa, wanda hakan zai kawo karshensa da ma jam'iyyar PDP.”

Sanatan na yankin Arewacin Adamawa ya jefa wannan barazana na shirya manakisa ne a zaben da za ayi ga gwamna mai-ci da jam’iyyar PDP da ta karbi mulki a jihar Arewa maso Gabashin kasar bana.

Tun ba yau ba dai ake samun irin wannan rikici tsakanin sabon Sanatan da gwamnan na Adamawa. Elisha Abbo wanda ya yi suna bayan zargin mari wata mata ya na ganin Fintiri na shirin rusa PDP.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel