Adadin jaruman Kannywood da suka bi doka, da kuma wadanda suka yi tawaye ga hukumar tace fina-finai
- Yayin da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta shafe tsawon sati hudu ta na kokarin tantance jaruman kungiyar
- Wasu daga cikin jaruman da yawa sun nuna tawayensu akan abinda hukumar tace fina-finan take yi, inda suka yi kunnen uwar shegu suka ki zuwa a tantance su
- Hakan ya sanya muka samo muku sunayen jaruman da suka barranta kansu da hukumar tace fina-finan
A makon jiya ne dai wa'adin da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta diba domin tantance masu sana'ar shirya fina-finai a jihar ya cika, lamarin da ya kawo karshen shirin tantance masu sha'awar yin sana'arsu da lasisi daga hukuma.
Rukunin masu sana'ar da hukumar ta sanar da cewa za'a tantance sun hada da jarumai, mawaka, marubuta, darektoci, furodusoshi, masu daukar hoto da tacewa da dai sauransu.
An shafe tsawon sati hudu ana gudanar da tantancewar amma abinda ya fi jan hankalin mutane shine, wadanne manyan jarumai ne da darektoci suka gabatar da kansu domin a tantance su da kuma wadanda suka barranta kansu da tsarin?
A wani kiyasi da jaridar northflix.ng ta wallafa, ta ce mutane 600 sun yi rijista a matsayin jarumai, 77 a matsayin furodusoshi, 76 a matsayin darektoci, marubuta 40 sai kuma mutum 30 da suka yi rijista a matsayin masu daukar hoto. Sai dai kuma alkaluman basu hada da na mawaka ba.
Jaridar ta ce kusan dukkan manyan fitattun jarumai mata sun je an tantance su, in banda wasu fitattun jarumai da suka hada da Rahama Sadau, Aisha Tsamiya, Fati Washa, Hadiza Gabon da Nafisa Abdullahi. An ce wasu daga cikinsu sun kira tare da bayar da uzurinsu na rashin halartar tantancewar.
KU KARANTA: Kullu Nafsin Za'ikatul Maut: Ladani ya mutu a Masallaci yayin da yake jira lokaci yayi ya kira sallar asuba
Jarumi Alasan Kwalle ya shaida wa wakilin northflix.ng cewa Rahama Sadau, Fati Washa, Hadiza Gabon, Nafisa Abdullahi da Ali Jita sun kira tare da bayar da uzurin rashin ganinsu yayin tantancewar. Hakan yake nuna cewa suna tare da tsarin tantancewar.
Haka zalika, akwai wasu fitattu a masana'antar ta Kannywood da tun farko suka barranta kansu da tsarin tantancewar, daga cikin wadannan jarumai akwai Adam A Zango, Sani Musa Danja, Mustapha Naburuska, Falalu A Dorayi, Yakubu Mohammed, Aminu Saira, Sunusi Oscar 442, Nazir Ahmad, Aminu Alan Waka, Nazir M Ahmad (Sarkin wakar San Kano), Misbahu M Ahmad, Baban Cinedu, Nuhu Abdullahi, Abdul Amat Mai Kwashewa, Nasiru Gwangwazo, Nazifi Asnaniq da dai sauran wasu daga cikin 'yan masana'antar ta Kannywood da sukai bara'a da wannan tsari na tantancewa da hukumar fina-finai ta kawo. Kamar dai yadda jaridar northflix ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng