Jihar Bauchi: An kama ‘Yan fashi da masu garkuwa da manyan masu laifi

Jihar Bauchi: An kama ‘Yan fashi da masu garkuwa da manyan masu laifi

‘Yan sandan jihar Bauchi sun kama mutane 185 da laifin fashin da makami, da kuma masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi. Daga ciki har da masu barna su na fakewa da sunan gwamna.

Jami’an tsaron sun damke wadannan masu mugun ta’adi a jihar ne kuma sun gabatar da su gaban jama'a a babban Hedikwatar ‘yan sanda da ke Garin Bauchi a Ranar Litinin, 30 ga Watan Satumban 2019.

Daga cikin wadanda aka kama akwai mutane biyu da su ka rika damfarar jama’a da sunan mai girma gwamna Bala Abdulkadir Muhammed. Kwamishinan ‘yan Sanda Habu Sani ya bayyana wannan.

Habu Sani yake cewa wani daga cikin masu laifin mai suna Sukni Zakka ya rika yaudarar mutane a matsayin cewa shi ne Hadimin gwamnan Bauchi, yayin da Iliyasu Ibrahim ya fakewa da sunan gwamna.

CP Sani yace wadannan rikakkun masu laifi da ake zargi sun rika damfarar mutane ne ta wayar tarho inda su ka yi awon gaba da Naira miliyan 37 a lokacin da ake jigilar aikin Hajjin shekarar bana.

KU KARANTA: DSS ta kama babban Darektan da EFCC ta ke nema tun 2015

Sukni Zakka ya kan yi waya ne da mutane da nufin shi ne Mai ba gwamna shawara, inda daga nan yake hada su da gwamnan na bogi su nemi kujerun aikin Hajji a kan kusan rabin ainihin kudin kujera.

Cikin mutum 185 da aka kama, an maka akalla 138 zuwa kotu inda sauran 47 su ke tsare yayin da ake cigaba da bincke inji Kwamishina. Sauran wanda aka kama sun hada barayin shanu da masu satar mutane.

Iliyasu Ibrahim mai shekara 33 da ke zama a Jos, yace Abokinsa Sukni Zakka ne ya daura shi a kan wannan hanya, ya ce: “Na nuna masa cewa ina jin tsoro, amma ya nace cewa ka da in wani damu.”

“Idan shi PA din ya samu mutanen da zai yi magana da su, sai ya kira ni a Bauchi daga Jos inda na ke waya da su tamkar ni ne gwamna, ba na labe muryata, sai kuma in fadawa mutanen za su tafi Hajji.”

Kudin kujerar Hajji miliyan 1.5 ne, amma wadannan mutane su karbi N600, 000 daga wajen mutane 9 a kan za a nema masu kujerun gwamnati. Sannan sun karbi N15, 000 a hannun mutane 28.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel