Yan majalisar dokokin jihar Sokoto na APC 2 sun lallasa yan PDP a kotun zabe

Yan majalisar dokokin jihar Sokoto na APC 2 sun lallasa yan PDP a kotun zabe

Kotun sauraron kararrakin zabe na majalisar dokokin jiha da ke zama a Sokoto, a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, ta jaddada zaben mambobin majalisar dokokin jihar Sokoto, da ke wakiltan mazabar Gada ta yamma, Hon. Kabiru Dauda da mai wakiltan mazabar Rabah, Hon. Abubakar Zakari.

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019, a mazabar Gada ta yamma, Hon. Garba Yakubu Tsitse ne ya kalubalanci kaddamar da Dauda na jam’iyyar All Progressives Congress ( APC) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hakazalika, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaben mazabar Rabah, Hon. Abubakar Gandi ya kalubalanci kaddamar da Zakari na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

A kararrakinsu, yan takarar sun yi zargin cewa wadanda ake karan basu samu mafi yawan kuri’un da aka kada bisa doka ba, sannan cewa zaben bai gudana daidai da dokar zabe na 2010 ba, da kuma tsarin jadawalin INEC na zaben 2019 ba.

KU KARANTA KUMA: Zan jingine kariyana domin a bincike ni, inji Osinbajo

Da yake yanke hukunci, Shugaban kotun zaben, Justis Ubale Yusuf, yace dukkanin kararrakin basu da inganci.

Yayi bayanin cewa masu karar sun gaza tabbatar da shari’arsu. Don haka Justis Yusuf yayi watsi da kararrakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel