Gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin karatun dalibai 242 zuwa kasahen ketare

Gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin karatun dalibai 242 zuwa kasahen ketare

Gidauniyar Kwankwasiyya ta kara jaddada kudirinta na bawa harkar ilimin matasa, da inganta rayuwar zawarawa da marasa karfi fifiko a jihar Kano.

Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ne ya sanar da hakan ranar Talata yayin bikin bita ga dalibai 242 da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyinsu domin zuwa karatu kasar Indiya da Sudan.

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa 234 daga cikin daliban zasu tafi kasar Indiya yayin da 8 zasu tafi kasar Sudan.

Dalibai 97 zasu yi karatu ne a jami'ar Sharda da ke kasar Indiya. A jami'ar Sharda ne Mubarak, dan Kwankwaso ya yi karatun jami'a.

Abba Kabir Yusuf ya ce wannan shine karo na farko da wata kungiya ko gidauniya a Najeriya ta taba daukan nauyin karatu da yawansu ya kai adadin da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyi.

DUBA WANNAN: Hukumar NDLEA ta kama dilolin kayan maye a hedikwatar jam'iyyar APC a Jigawa

Ya bukaci daliban da su kasance jakadu nagari ga jihar Kano da Najeriya a kasashen da zasu je domin yin karatun.

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, ya ce wannan ba shine karo na karshe da gidauniyar Kwankwasiyya za ta dauki nauyin dalibai zuwa kara karatu a kasashen ketare ba, tare da bayyana cewa gidauniyar na cigaba da kokarin ganin yadda za ta fadada aiyukanta na taimakon jama'a.

Gidauniyar ta dauke wa daliban nauyin tikitin dawowarsu gida, samar musu muhalli, biyan kudin makaranta da basu alawus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng