Sanata Sani ya roki Shugaba Buhari ya sa baki a rikicin ‘Yan Sandan Najeriya

Sanata Sani ya roki Shugaba Buhari ya sa baki a rikicin ‘Yan Sandan Najeriya

Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya yi kira ga Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sasanta rikicin da ake yi a gidan ‘yan sanda.

Sanata Shehu Sani ya nemi shugaban kasa ya yi maza ya sa baki domin kawo karshen rikicin da ake ta faman yi tsakanin hukumar ‘yan sanda da kwamishon da ke kula da jami’an tsaron kasar.

An samu sabani ne tsakanin Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, da kuma hukumar PSC mai kula da harkokin ‘yan sanda a Najeriya kan daukar sababbin ma’aikata 10,000.

Kowa ya na ikirarin cewa shi ne ya ke da ikon daukar aiki a gidan ‘yan sanda wanda hakan ya jawo babban sabani tsakanin IGP da hukumar PSC da tsohon IGP, Musiliu Smith ya ke jagoranta.

KU KARANTA: An kama wata tsohuwa da laifin saida wayar salular sata

Sani ya yi magana a game da wannan takaddama da ya ki ci ya kuma gagara cinyewa inda ya nemi shugaban kasa ya yi gaggawar sa baki domin kawo karshen wannan matsala da ake samu.

Kwamred Sani a shafinsa na Tuwita ya ce: “Shugaban kasa ya hanzarta ya shawo kan sabanin da ake samu tsakanin Dakarun ‘Yan Sanda da Hukumar PSC kan batun daukar ma’aikatan nan.”

Fadar shugaban kasar dai ba ta tanka wannan magana na tsohon Sanatan APC ba. Sai dai idan ba ku manta ba, a kwanakin baya shugaban kasa Buhari ya zauna da IGP da kuma Shugaban PSC.

Shugaban kasa ya gana da shugabannin ‘yan sandan ne domin ganin an kawo karshen rikicin da ake yi. Buhari ya nemi Musiliu Smith ya yi abin da ya dace bayan kukan da PSC ta kai masa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel