Wasu kishiyoyi sun lakada wa mijinsu dukan tsiya bayan yayi kokarin auren mata ta uku

Wasu kishiyoyi sun lakada wa mijinsu dukan tsiya bayan yayi kokarin auren mata ta uku

Kamar yadda kuka sani wasu mazan na da karfin sha’awa wanda hakan kan sanya su bukatar tara mata kamar dukiya. Wani mutumin kaar Indiya, Dinesh, ya fada a wannan rukuni, inda ya hadu da gamonsa bayan yayi kokarin sake auren mata ta uku ba bisa ka’ida ba.

An tattaro cewa ya sha dukan tsiya a hannun matansa a lokacin da yayi kokarin auren mata ta uku. A lura cewa ya yi auren fari a shekarar 2016 kafin ya fara kokarin auren ta uku a 2019.

Daily Mail ta ruwaito cewa Dinesh na cin zarafin matansa biyu ta hanyar dukkan su wannan dalilin yasa suka koma gidan iyayensu.

Sai dai matan biyu da ya aura da fari ba su san cewa mutum guda suka aura ba saboda a tunaninsu Dinesh mata daya kawai ya aura.

Wasu kishiyoyi sun lakada wa mijinsu dukan tsiya bayan yayi kokarin auren mata ta uku
Wasu kishiyoyi sun lakada wa mijinsu dukan tsiya bayan yayi kokarin auren mata ta uku
Asali: UGC

Amma da suka gano cewa mijinsu mata biyu ya aura kuma yana shirin kara auren ta uku, sai suka dauki mummunan mataki a kan sa.

A bidiyon an gano matan biyu suna bin Danesh shi kuma yana kokarin guduwa.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya koka bayan tsallake rijiya da baya, yace wani malamin addini yayi masa biza na bogi

Wasu mutane su ma sun taya matan dukkansa kafin daga bisani aka mika shi hannun yan sanda.

A lura cewa a shekarar 1956 ne addinin Hindu ta haramta namiji ya auri mata sama da guda daya amma musulmi suna iya auren har mata hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel