Ina nan da raina ban mutu ba - Maryam Yahaya

Ina nan da raina ban mutu ba - Maryam Yahaya

Fitacciyar jarumar Kannywood wacce tauraronta ke kan ganiyar hasakawa bayan ta shiga masana'atar shirya fina-finan da kafar dama, Maryam Yahaya, ta yi watsi da jita-jitan da ke yawo a shafukan sadarwa na cewa ta mutu.

A cewar Maryam tana nan da ranta bata mutu ba kuma tana cikin koshin lafiya. Tace wasu ne suka yada hakan a shafin Facebook alhalin ita bata ma amfani da kowani shafi a Facebook din.

Ta kuma gargadi wadannan suke jaza mata wannan alkaba’i, alhalin tana nan da ranta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da rubutu da ta wallafa shafinta na Instagram.

KU KARANTA KUMA: Madalla: An kama mutane 3 kan garkuwa da yaran Shugaban karamar hukuma a Katsina

Ga yadda ta wallafa a shafin nata: “Aslm..masoyana ina muka barka da warhaka, naji anata jita jita akan cewa ni Maryam yahaya na MUTU toh ni Maryam yahaya ban mutuba ina nan da raina kuma cikin koshin lafiya..! Spreading rumors and gossip is incredibly dangerous.it destroys reputation,breaks Down relationships and causes mayhem in someone’s life. it’s so common today because so many have lost basic decency and wouldn’t bat an eyelid mass texting such messages.be careful!”.

Ga bidiyon kuma a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel