Deepika Padukone, Taylor Swift, da sauran Matan da aka sallamawa a kyau
Mun tattaro maku jerin Matan da ake yawan maganar baiwar kyawun da su ke da shi. An tsakuro biyar daga cikin mafi shararrun matan da Duniya ta sallamawa surar da dirin da su ke da shi.
Jaridar kasar waje ta Wise Toast ce ta faro kawo jerin kyawawan mata 10 inda mu ka zabo 5 da su ka fi fice daga cikinsu. Akwai ‘yan wasan fim da da Mawaka da sauran ‘yan wasa a jeringiyar.
1. Deepika Padukone
‘Yar wasa Deepika Padukone ta na cikin matan da su ka fi kowa kyau a Duniya. Bugu da kari, duk ‘yan wasan fim na Indiya babu mai karbar albashin wannan zankadediyar kyakkyawar Mata.
2. Candice Swanepoel
An haifi Candice ne a shekarar 1988 kuma asalin ta Mutumiyar Kudancin Afrika ce. Candice ta yi suna ne a kamfanin Victoria Secret. Albashin wannan kyakkyawar Baiwar Allah sai ya ka tsoro.
3. Taylor Swift
Taylor Swift ‘yar wasan kasar Amurka ce wanda ta shahara wajen wake-wake wanda ya jawo mata suna da daukaka a ko ina. Ban da tashe da Mawakiyar ta yi, ta na kuma da ‘dan karen kyau.
KU KARANTA: Jerin manyan Kasashen da su ka fi kowane arziki a Afrika
4. Aishwarya Rai
Aishwarya Rai ta na cikin masu kyau a Duniya har gobe. Shekaru 25 da su ka wuce ne ta lashe gasar sarauniyar kyau. ‘Yar wasar fim din Indiyar mai shekaru 41 ta zarce sa’o’in ta wajen kyau.
5. Scarlett Johansson
Scarlett Johansson ta shiga cikin sahun kyawawan matan da ke da rai yanzu a Duniya. Johansson ‘yar wasar kwaikwayo ce, kuma Mawakiya, sannan kuma kyakkyawar gaske.
A iya samun tarin mutane da su ka fi wadannan mata da mu ka kawo kyau. Sai dai wadannan din su na cikin manyan Taurari wanda Duniya su ka san su, kuma su ma su ka san Duniyar da kyau.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng