Madalla: An kama mutane 3 kan garkuwa da yaran Shugaban karamar hukuma a Katsina

Madalla: An kama mutane 3 kan garkuwa da yaran Shugaban karamar hukuma a Katsina

Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ke da nasaba da garkuwa da yaran Shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Matazu da ke jihar, Kabiru Matazu guda biyu.

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya sanar da kamun a hedkwatar rundunar da ke Katsina a ranar Talata, 18 ga watan Satumba.

Masu laifin sun kasance mambobin kungiyar yan bindigan da suka kai mamaya gidan Shugaban karamar hukumar, inda suka kasha masu gadinsa da kuma garkuwa da yaransa maza biyu araar Laraba da ya gabata.

A cewar wata majiya na iyalin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace kwanan nan ne daya daga cikin yaran da aka sace ya kammala makarantar sakandare.

Kakakin yan sandan, wanda ya tabbatar da kamun masu laifin, bai bayyana sunayensu ba.

Wata majiya na iyalinn, wanda ya nemi a sakayya sunansa, ya fada ma majiyarmu cewa masu garkuwan sun kira iyalin sannan sun nemi a basu kudin fansa naira miliyan 50 kafin su saki yaran.

KU KARANTA KUMA: Na rasa yadda zanyi da ita saboda har cikin dakin mu na sunnah Madina take kawo gardi tayi zina dashi - Wani mutumi ya koka

“Har yanzu muna rokon masu garkuwan; da farko sun bukaci naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa amma mun fada masu bamu da wannan kudin. Har yanzu yaran na a hannunsu sannan muna addu’a kan Allah yasa su sake su kan lokaci,” inji majiyar.

Sai dai, kakakin yan sandan ya bayyana cewa bashi da masani akan kudin fansan da suka bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel