Kaho mai tsawon inci 4 ya fito a kan wani mutum bayan ya yi hatsari
Kaho mai tsawon inci hudu ya fito ma wani mutumin kasar Indiya mai shekaru 74, Shyam Lal Yadav, bayan ya ji rauni a kai cikin shekarar 2014.
A kwanan nan ne Likitoci a asibitin Bhagyoday Tirth da ke birnin Sagar, Indiya suka cire kahon daga kan Yadav.
Yadav, wanda ya kasance manomi daga kauyen Rahli da ke Madhya Pradesh, yaji rauni a shekarar 2014 a kansa inda hakan yayi sanadiyar tsirowar kaho a kan nasa, Daily Mail ta ruwaito.
Tsiron wanda a kasafai akee ganin irinsa ba ya fi fitowa mutanen da shekarunsu ya jawato tsoffi.
Tsawon shekaru da dama Mista Yadav na ta haske tsiron, har sai da abun ya fara girma ba kama hannun yaro sannan manomin ya nemi ayi masa tiyata.
Wani likita, Dr Vishal Gajbhiye, wanda ya yi masa tiyatan yace, "Kimanin shekaru biyar da suka gabata mara lafiyan ya ji rauni a kansa wanda daga bisani ya fara tsirowa. da fari, ya yi wasti da hakan tnda baya damunsa. sannan ya kan je wajen wanzamai su yanke masa.
KU KARANTA KUMA: Hukumar FRSC ta kulla wata yarjejeniya da kamfanin Dangote
"Amma lokcin da tsiron yayi karfi sannan ya ci gaba da girma, sai ya tunkari asibiti a Sagar."
Gajbhiye ya bayyana cewa yayinda ake iya cire tsiron, akwai bukatar kula da halin da kasan ke ciki. yayinda aka yanke tsiron, har yanzu likitoci basu san abunda ya haddasa shi ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng