Wata mata ta haifi 'yaya 4 a Bauchi, ta roki gwamna ya bata aiki

Wata mata ta haifi 'yaya 4 a Bauchi, ta roki gwamna ya bata aiki

Wata mata 'yar asalin karamar hukumar Tafawa Balewa da ta haifi 'ya'ya hudu ta roki gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammded, ya taimaka ya bata aiki domin ta samu damar daukan nauyin 'ya'yan da ta haifa.

Matar, Nyarum Luka Bot Balewa, mai shekaru 41, ta ce duk da haihuwar 'ya'yan ya saka musu farinciki ita da mijinta saboda sun shafe shekaru 15 babu haihuwa, daukan dawainiyar yaran abu ne mai wuya.

"Daukan nauyin wadannan 'ya'ya ba abu ne mai sauki ba, saboda yanzu mijina bashi da wani aiki, ya yi ritaya. Mu na da wasu yaran da suke zuwa makaranta.

"ba abu ne mai sauki ba. Ina neman taimakon gwamnati ta bani aiki. Ina da takardar shaidar kammala karatun difloma a bangaren kula da lafiyar muhalli. Su taimaka su bani aiki don na taimaki mijina," a cewar matar.

Nyarum, wacce ta kammala karatu a makarantar kwalejin kimiyyar lafiya da ke garin Ningi a jihar Bauchi, ta haifi 'ya'ya uku mata da yaro daya namiji a ranar 3 ga watan Yuli a asibitin Birgham da ke jihar Filato.

DUBA WANNAN: Maganin damfara: Hanyoyi 5 da mutum zai gane kudin jabu

Mijin Nyarum, Luka Bot Balewa, wanda ya yi ritaya a matsayin ma'aikacin asibitin koyarwa na jami'ar Tafawa Balewa a shekarar 2018, ya ce daukan dawainiyar 'ya'ya hudu rigis ba abu ne mai sauki ba.

"Ba abu ne mai sauki ba, saboda dole ake bawa yaran madara kuma karamin gwangwanin madara ma N2,150 muke sayansa yanzu.

"Jariran na shan karamin gwangwanin madara kowacce rana bayan nonon mahaifiyarsu. Ita kanta mahaifiyarsu tana bukatar ta ci abinci mai kyau," a cewar Luka.

Luka ya roki gwamnan jihar Bauchi da sauran 'yan Najeriya masu hali da su kawo musu agaji tare da bayyana cewa har yanzu kudin fanshonsa basu fito ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel