NECO ta rike sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 a Neja saboda bashi
Hukumar jarrabawar NECO ta rike sakamakon jarrabawar dalibai sama da 30,000 a makarantun gwamnatin jihar Neja, saboda rashin biyan kudin jarrabawarsu da gwamnatin jihar bata yi ba.
A yanzu haka daliban basu samu damar duba sakamakon jarrabawarsu ta NECO ba wanda aka saki a ranar 27 ga watan Agusta, 2019.
Daliban makarantun sakandare sun isa ga maneman labarai, inda suka koka akan rashin samun damar mallakar sakamakon jarrabawarsu domin su halarci tantancewar post-UTME na shiga jami’o’in da suke so.
Gwamnatin jihar ta yarda cewar hukumar jarrabawar na binta bashin naira miliyan 400, inda ta kara da cewar sun biya naira miliyan 150.
Sakataren din-din-din na ma’aikatar ilimi na jihar Neja, Abubakar Aliyu, a lokacin da aka tuntube shi a jiya Litinin, 16 ga watan Satumba, ya yarda cewar hukumar na binsu bashi amma ya roke ta da ta dua lamarin domin ba daliban damar mallakar sakamakonsu, musamman wadanda suka isa zuwa tantancewar post-UTME.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a hanyar babban titin Delta
Yace jihar bata da isasshen kudin biyan NECO a lokaci guda, inda ya bayar da tabbacin cewa za su biya a duk lokacin da aka samu kudi, inda ya kara da cewa idan ba a saki sakamakon ba kafin karshen ranar Litinin din, za su duba wasu hanyoyi na biyan bashin.
Ya kara da cewa daraktocin ma’aikatar sun gana da hukumar NECO a ranar Litinin din.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng