Dalilin da yasa ba a saki Naziru Sarkin waka daga gidan yari ba – Lauyan sa

Dalilin da yasa ba a saki Naziru Sarkin waka daga gidan yari ba – Lauyan sa

Jama’a na ci gaba da zuba ido tare da sanya ran sakin Naziru M. Ahmad, wanda aka fi said a Sarkin Wakar Sarkin Kano daga inda yake tsare, a gida kurkukun Kano bayan ya gaza cika sharuddan belin da kotu ta shimfida masa.

Rundunar yan sandan jihar Kano ce ta gurfanar da mawakin a gaban kotu kan zargin fitar da wasu wakoki ba bisa ka’ida ba.

Lauyan mawakin, Barista Sadiq Sabo Kurawa ya yi tsokaci akan halin da ake ciki a yanzu, inda yace: “Dalilin da yasa ba a sako shi ba tun jiya Alhamis, shi ne rashin kammala tantance sharudan da kotu ta gindaya masa".

Ya kuma ce tun jiya: "Jami'in kotu da zai tantance sahihancin abubuwan da kotun ke bukata ya riga ya kammala aikinsa".

Wannan na nufin idan alkalin ya amince da cewa ya cika sharuddan, yana iya sako shi cikin yinin Jumma'a, 13 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Awanni kadan da dawowar 'yan Najeriya, 'yan kasar Afrika ta Kudu sun koma kashe 'yan Pakistan

Amma idan hakan bai samu ba, Naziru Sarkin Waka na iya shafe kwanakin karshen mako a gidan yari har sai ya gamsar da alkali cewa dukkan sharuddan da aka shimfida ya samar da su.

Amma lauyan nasa na da karfin gwuiwar haka ba zai faru ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel