Kuma dai: 'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban karamar hukuma a Katsina, sun sace yaransa 2

Kuma dai: 'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban karamar hukuma a Katsina, sun sace yaransa 2

Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kisan wani mutum guda daya tare da sace wasu yara guda biyu yayin da suka kai hari gidan shugaban karamar hukumar Matazu a jihar Katsina.

Kai harin ya zama tamkar koma baya ga yunkurin yin sulhu da 'yan bindiga da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ke yi.

Karamar hukumar Matazu na daga cikin kananan hukumomin jihar Katsina guda takwas da hare-haren 'yan bindiga suka tsananta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce lamarin ya faru ne da da duku-dukun safiyar ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Ba lallai sulhu da 'yan bindiga ya yi tasiri ba - Gwamna Zakari Umaru

Ya ce mutumin da 'yan bindigar suka kashe mai suna Kabir Matazu yana aikin gadi ne a gidan shugaban karamar hukumar.

SP Isah ya ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da 'ya'yan shugaban karamar hukumar su biyu.

Kakakin ya bayyana cewa tuni rundunar 'yan sanda fara yunkurin kama 'yan bindigar tare da kubutar da yaran ta hanyar amfani da kayan bin sahu na fasahar zamani (tracker).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel