Daliba ta kashe kan ta bayan jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta saboda rashin 'kunzugu'

Daliba ta kashe kan ta bayan jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta saboda rashin 'kunzugu'

Rundunar 'yan sanda a kasar Kenya ta fara bincike a kan dalilin da yasa wata dalibar makarantar firamare mai shekaru 14 ta kashe kan ta saboda jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta.

Beatrice Chepkurui, mahaifiyar matashiyar, ta ce malamin dake koyar wa a makarantar ne ya kunyata diyarta bayan jinin al'ada ya bata mata kayan da ta je makaranta da su.

"Ba ta saka wani kunzugu ba kafin ta tafi makaranta, lamarin da yasa jinin al'adar ya bata mata kayanta bayan ya zuba. Malamin ya yi mata fada tare da bata umarnin ta fita daga ajinsu, ta saya a waje," a cewar Beatrice.

Hakan ne yasa Beatrice tare da wasu iyayen yara suka gudanar da zanga-zangar neman a kama malamin makarantar firamaren da ke garin Kabiangek, mai nisan kafa 270 daga Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Masu zanga-zanga a wajen makarantar na neman a kama malamin makarantar bisa kyarar matashiyar, lamarin da ya jawo ta kashe kan ta.

Wata jaridar kasar Kenya 'Daily Nation' ta rawaito cewa sai da 'yan sanda suka yi amfani barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar bayan sun rufe titi, lamarin da ya haddasa cunkuson ababen hawa tare da rufe makarantar.

DUBA WANNAN: 'Yan jarida sun hada gwuiwa da kungiyoyi domin bin diddigin alkawuran da El-Rufa'i ya dauka a Kaduna

A watan Yuni na shekarar 2017 ne gwamnatin kasar Kenya ta yi dokar cewa zata ke samar da audugar nade jinin al'ada kyauta ga daliban makarantun firamare.

Labarin mutuwar yarinyar yasa yanzu haka majalisar dokoki a kasar Kenya ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike a kan dalilin da yasa har yanzu dokar samar da audugar al'ada kyauta ga dalibai mata a makarantun firamare bata fara aiki ba.

Rift Valley, wani babban jami'in 'yan sanda a yankin da abin ya faru, ya ce suna gudanar da bincike a kan faruwar lamarin tare da yin kira ga iyayen yara da su zama masu kusantar 'ya'yansu domin sanin halin da suke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel