Cristiano Ronaldo ya yi ruwan kwallaye a wasan Portugal da kasar Lithuania

Cristiano Ronaldo ya yi ruwan kwallaye a wasan Portugal da kasar Lithuania

Babban ‘Dan wasan Duniya, Cristiano Ronaldo ya zuba kwallaye har hudu a raga a lokacin da kasarsa ta hadu da Lithuania a wasan zuwa gasar cin kofin Nahiyar Turai da za ayi a 2020.

‘Dan wasan gaban na Portugal ya yi wa Lithuania rubdugun ne a wasan da aka tashi 5-1. Cristiano Ronaldo ya tashi wannan wasa da kwallaye 24 a cikin wasannin zuwa gasar Euro na Turai.

Ronaldo ya doke tarihin Robbie Keane wanda kafin yanzu yake da kwallaye 23 da ya ci wajen karawa zuwa babbar gasar kasashen Turai. Portugal ta yi wa Lithuania kaca-kaca a wasan.

Kwallaye uku da Ronaldo ya ci a mintuna 15 su ka sa Keane ya fita daga na farko wajen yawan kwallaye a littafin tarihin Turai. Bayan an dawo hutun rabin lokaci, Ronaldo ya kara kwallo guda.

KU KARANTA: Yadda shawarwari na su ka yi tasiri a kan Lionel Messi - inji Maradona

Ronaldo mai bugawa kungiyar Juventus ya fara ne da cin finariti bayan minti bakwai rak da take wasa. ‘Dan wasa William Carvalho shi ne ya ci wa Portugal kwallon karshe ana daf da tashi.

Abin da wasan yake nufi shi ne yanzu saura kwallaye 16 Ronaldo ya kamo Ali Daei wajen yawan kwallaye a kasa. Daei ya ci wa kasar Iran kwallaye 109 inda Ronaldo ya ke da 93 yanzu.

Lithuania ita ce kasa ta 40 da ta gamu da ta’adin Cristiano Ronaldo a kwallo. A cikin wasanni 160 da Ronaldo mai ballon d'or 5 ya bugawa kasarsa, ya zarce kowa wajen adadin kwallaye.

Idan ku na biye da mu, kun ji labari cewa an bayyana abin da Ronaldo yake karba a matsayin albashi a kasar Italiya. Duk gasar Seria A, babu wanda ya kamo kafarsa a wajen samun kudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel