Daukar ma’aikata 10,000: Ku yi watsi da jerin sunayen da NPF ta fitar – Hukumar yan sanda ga masu neman aiki

Daukar ma’aikata 10,000: Ku yi watsi da jerin sunayen da NPF ta fitar – Hukumar yan sanda ga masu neman aiki

Hukumar yan sanda ta bukaci masu neman aikin yan sanda da su yi watsi da jerin sunayen da rundunar yan sandan ta fitar.

A makon da ya gabata hukumar ta dakatar da tsarin daukar ma'aikatan wanda ya kai matakin tantance matsayin kiwon lafiya.

A cewar Majiyoyi, an sanar da dakatarwar ne bayan alamu sun nuna cewa shugabancin yan sandan na iya sauya sunayen da aka gabatar mata.

Har ila yau majiyoyin sun bayyana cewa shugabancin rundunan yan Sanda ta yanke shawaran amshe tsarin bayan shugaban hukumar, Alhaji Musiliu Smith ya ki amincewa da bin tsarin da shugabancin rundunan yan sandan ke so

Daga cikin kokarin hana shugabancin rundunan yan sandan, hukumar ta dakatar da tsarin ta kuma bayyana makoman wadanda ke neman aiki zasu san shwarar da aka yanke a karshen tattaunawa a wannan makon.

Shugabancin rundunan yan sandan duk da haka a ranar Talata ta saki sunayen wadanda suka kai matakin tantancewar kiwon lafiya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ta ziyarci shafin yanar gizon rundunan yan sanda don duba jerin sunaye mai dauke da batu: “2019 Medical Screening list” amman ba ta ga sunayen ba.

Duk kokarin da aka yi na karanta karin bayanai a shafin yanar gizon ya ki budewa.

Yayin da yake mayar da martani akan sunayen, hukumar a wani jawabin daga kakakin rundunar, Ikechukwu Ani a Abuja, ya shawarci wadanda ke neman aiki da su jira sunayen gaskiya daga gare ta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun bijirewa yan sanda, sun yi tattakin Ashura a Wuse

"Dukkan masu neman aikin wadanda suka rubuta jarabawa a ranar Asabar, 30 ga watan Agusta 2019 su jira sunayen gaske wanda za a sako bayan hukumomin sun tattauna," inji shi

Hukumar ta shawarci masu neman aiki da kada su ji tsoro da kuma yanke kauna kamar yanda za a kare musu hakkokin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel