Lionel Messi zai iya barin Barcelona a badi – Inji Maria Bartomeu

Lionel Messi zai iya barin Barcelona a badi – Inji Maria Bartomeu

Mun samu labari a Ranar Juma’a cewa shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu, ya yi magana game da babban Tauraron Duniya Lionel Messi wanda ya ke taka leda a kulob din.

Josep Maria Bartomeu ya bayyana cewa babu abin daga hankali game da zaman Lionel Messi a Barcelona. Shugaban kulob din ya yi wannan bayani ne Ranar 6 ga Watan Satumba, 2019.

Da Josep Bartomeu ya ke magana da gidan talabijin na Bacelona a shekaran jiyar, sai ya ke cewa: “Leo Messi ya na da kwantiragi har kakar 2020 zuwa 2021, amma ‘dan kwallon ya na iya tashi.”

Mista Josep Bartomeu ya ce: “Leo Messi ya na iya barin Barcelona kafin kakarsa ta karshe.” Kungiyar kwallon kafan na Barcelona ta nuna cewa ba ta jin wani dar-dar kan ‘dan wasan na ta.

KU KARANTA: Akwai alamun a samu abokantaka tsakanin Messi da Ronaldo

‘Dan kwallon na Duniya wanda ya lashe Ballon D’or sau biyar a Sifen ya rattaba hannu ne a kan wani sabon kwantiragi a Barcelona a 2017. Messi ya hannu kan kwangilar shekaru hudu.

Duk da cewa sai a shekarar 2020 zuwa 2021 ne kwangilar ‘dan wasan za ta kare da. Shugaban kungiyar, Maria Bartomeu, ya na ganin cewa ‘dan wasan ya na iya tashi inda ya so kafin nan.

A bara ne babban Abokin hamayyar Messi watau Ronaldo ya bar Madrid inda ya koma Juventus. Idan har Messi zai bar Barcelona inda ya shafe shekaru, irunsu Man City za su iya nemansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel