Neman iko kan daukar aikin 'Yan Sanda ya kawo rigima tsakanin NPF da PSC

Neman iko kan daukar aikin 'Yan Sanda ya kawo rigima tsakanin NPF da PSC

Mun ji labari cewa kokarin nuna iko da isa wajen daukar Dakarun ‘yan sanda aiki ya sa an samu matsala tsakanin hukumar ‘yan sandan Najeriya da kuma Takwararta watau hukumar PSC.

Maganar daukar ma’aikata 10, 000 da za ayi a gidan ‘yan sanda ya dauki wani sabon salo bayan da Sufeta Janar na ‘Yan sanda, Mohammed Adamu, ya fitar da sunayen wadanda za a dauka aikin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar PSC mai kula da harkar ‘yan sandan kasar ta fito ta bayyana cewa ta dakatar da shirin da ake yi na daukar aikin domin ita ce ke da alhakin haka.

Shugaban PSC, Alhaji Musiliu Smith, ya iya samun labarin fitar da sunayen wadanda za a dauka ne a lokacin da su ke ganawa da kwamitin harkokin ‘yan sanda na majalisar wakilan tarayya.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, Musliu Smith ya yi matukar mamakin jin cewa Sufetan ‘yan sanda ya fito da sunayen wadanda za a dauka aiki lokacin da ‘yan majalisar su ka kira su taro.

‘Yan majalisar tarayya sun zaunar da Musliu Smith da IGP Mohammed Adamu, da kuma Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Maigari, domin sasanta rikicin da ya shiga tsakanin su.

KU KARANTA: Jami'in 'Dan Sanda ya mutu wajen binciken Wadume

A Ranar Juma’ar da ta gabata, PSC ta ce an tsaida shirin daukar sababbin ma’aikata a gidan ‘yan sanda. Bayan kwana biyu kurum sai aka ji IGP Adamu a Garin Ibadan yana musanya wannan maganar.

Hukumar ‘yan sanda na NPF tayi gaba ta fitar da jerin wadanda za su shiga aikin tsaro a kasar. Kafin a je ko ina, Kakakin hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya fito ya ce jerin bogi ne aka fitar ba komai ba.

PSC ta yi watsi da sunayen da hukumar ta fitar saboda a cewarta, babu hannunta a ciki. Wannan ya sa dole NPF ta janye sunayen wadannan mutane da ta fitar wanda IGP ya nuna bai san da zamansu ba.

Babban Sakataren hukumar PSC, Maurice Mberi, ya bayyana cewa Musliu Smith zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari game da wannan matsala, don haka aka nemi masu neman aikin su dakata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel