Jerin masu ban dariyan da su ka zarce sa’o’insu arziki a yanzu

Jerin masu ban dariyan da su ka zarce sa’o’insu arziki a yanzu

Kwanan nan Mujallar nan ta Forbes ta fitar da jerin masu wasan barkwanci da su ke kan gaba wajen arziki. Legit.ng Hausa ta tsakuro maku 5 daga cikin wadannan manyan Taurarin Duniya.

Masu ban dariyar su ka san samu kudi ne ta hanyar yin wasanni, shiri a gidan talabijin ko kuma rubuce-rubuce. A cikin manyan Taurarin, babu wani mutumin kasar Najeriya da ya samu shiga.

1. Kevin Hart: Dala miliyan $59

Kevin Hart wanda ya samu kansa cikin ce-ce-ku-ce kwanan nan bai da sa’a a cikin masu wasan barkwanci. A cikin wannan shekarar ya samu abin da ya kai Dala miliyan 59 wajen wasanninsa.

2. Jerry Seinfeld: Dala miliyan $41

Jerry Seinfeld ne ya zo na biyu cikin masu samun kudi wasan ban dariya a Duniya. A bana Sienfeld ya samu fam miliyan 41. Wannan kadan ne domin a 2016, samunsa ya haura Dala miliyan 57.

KU KARANTA: Abin da ya sa Ahmed Musa ya zama Kyaftin din Najeriya

3. Jim Gaffigan: Dala miliyan $30

Jim Gaffigan ya zo na uku a wannan jeri na Forbes a shekarar nan. A shekarar nan Gaffigan ya yi sababbin wasanni irin su Noble Ape da Quality Time wanda su ka sa ya tashi da Dala miliyan 30.

4. Trevor Noah: Dala miliyan 28

Noah shi ne ke bin kadin Gaffigan bayan ya tashi da fam Dala miliyan 28 a asusunsa wannan shekarar. Noah ya kan yi shiri a gidan Talabijin kuma ya samu kudi da littafinsa Born a Crime.

5. Sebastian Maniscalco: Dala miliyan 26

Maniscalco yana cikin Taurarin Amurka da su ka yi kudi da ban dariya. Ya fito a shirin barkwanci na Wild West kuma kwanan nan ya fitar da wasu shirye-shiryen da su ka jawo masa miliyan 26.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng