Siyasar 2023: Hotunan takarar shugaban kasa na El-Rufai da Oshiomole sun bayyana
A wani mataki mai daukan hankali, hotunan yakin neman zabe na takarar shugabancin kasar nan dauke da hoton shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole da gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai sun bayyana.
Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa fastocin sun fara yawo a yanzu haka a jahar Legas, inda tace ta yi ido hudu da ire iren hotunan nan a unguwar Surulere ta jahar Legas, da kuma yankin dake kusa da dandalin wasa na jahar Legas.
KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun bude ma kiristoci wuta a coci a Taraba, sun kashe mutane 3
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a cikin wannan hoto dai an buga hoton shugaban APC, kuma tsohon gwamnan jahar Edo, Adams Aliyu Oshiomole da sunan dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, yayin da hoton Malam Nasiru El-Rufai yake dauke da sunan dan takarar mataimakin shugaban kasa.
Haka zalika wannan fasta yana dauke da wasu halaye guda 8 wadanda mabuga hotunan suka ce sune suka sanya mutanen biyu suka fi cancanta su tsaya takarar shugaban kasa da mataimaki a zaben 2023 domin gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Daga cikin wadannan halaye da mabuga fastocin suka buga akwai:
- Mutane biyu da suke da halin biyayya
- Mutane biyu da suke da mutunci
- Mutane biyu masu son zaman lafiya
- Mutane biyu da suka amince da Dimukradiyya
- Mutane biyu da suke da gaskiya da rikon amana
- Mutane biyu da suka yarda da sauya fasalin Najeriya
- Mutane biyu da basu yarda da siyasar ubangida ba
- Mutane biyu da suka yarda da hadin kan Najeriya
Daga karshe an rubuta sunan wata kungiya mai suna ‘Miyatti Allah Cattle Breeders Association’ a matsayin wadanda suka buga wadannan fastoci.
Dama dai masana siyasar Najeriya na has ashen gwamnan jahar Kaduna zai iya fitowa takarar shugaban kasa, amma bait aba tabbatar da haka a fili ba, kuma ko a yanzu bai ce komai game da wannan hoto ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng