An kama wata mata da ta siyar da dan sata akan N300,000 a jihar Neja

An kama wata mata da ta siyar da dan sata akan N300,000 a jihar Neja

Rundunar yan sandan jihar Neja ta cafke wata mata mai suna Bose Isaac, bisa laifi siyar da wani yaro da ta sace akan naira N300,000.

Wacce ake zargin tayi shirin tserewa a lokacin da aka yi yunkurin kama ta bayan mahaifin yaron, Gambo Shua’ibu a kauyen Cikin-Gari ya kai korafi akan bacewar yaronsa a ranar 24 ga watan Agusta.

Kakakin rundunar yan sanda Reshen jihar Neja, Muhammad Abubakar, yace yan sandan sashin Kagara sun kama mai laifin. A cewar shi, Bose Isaac ta karbi bakin aikata laifin sace yaron da kuma kai shi wurin wata mata a jihar Ogun wacce tayi alkawarin bata kudi N300,000.

Mai laifin wacce ta yi ikirarin cewa ta bukaci kudin ne don biyan “bukatun iyalinta”, tace wacce ta siyi yaron bata cika mata alkawarin ba har yanzu.

KU KARANTA KUMA: Wadume ya yi kuskure da ya nemi mafaka a jihar Kano - Ganduje

Da aka tambaye ta ko menene dalilin da yasa ta siyar da dan wata, tace “shaidan ne ya tursasata da kuma talaucin da ke kasar wanda ya jefa ta cikin halin kakanikaye.”

Kakakin yan sandan ya cigaba da cewa yan sanda suna aiki dare da rana don ganin sun kama wacce ta siyi yaron yayinda suke kammala bincikenta don gurfanar da mai safaran a kotu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng