Dr. Isa Pantami ya rabawa Hukumomin NCC, NITDA, NIPOST, dsr, aikin gabansu

Dr. Isa Pantami ya rabawa Hukumomin NCC, NITDA, NIPOST, dsr, aikin gabansu

Ministan sadarwa Dr. Isa Ali Pantami, ya rabawa shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatarsa aikin da za su yi. Wannan ya shafi har da manyan Darektocin ma’aikatarsa.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto jiya, 1 ga Watan Satumba, 2019, Isa Pantami ya bayyana wannan ne a Hedikwatarsa a birnin tarayya Abuja inda yi kira ga CEO da Darektocin su tashi tsaye.

Dama can Ministan ya bayyana cewa za a sanyawa kowace ma’aikata aikin da ake so ta yi zuwa wani lokaci, inda za a rika bibiyan kokarin da kowane shugaba ya ke yi domin sauke nauyin da ke kansa.

1. Kamfanin Galaxy Backbone

Daga cikin aikin da aka ba wannan kamfani shi ne su gyara karfin layinsu da sauran ayyukan da su ke yi wa jama’a.

2. Hukumar NCC

Ma’aikatar sadarwa ta ba NCC lokaci ta kawo karshen matsalar rashin yi wa layukan waya cikakken rajista wanda hakan zai inganta matsalar rashin tsaro. An kuma nemi NCC ta duba yadda ake zaftarewa jama’a kundin hawa yanar gizo tare da rage farashin na data da kuma waya.

KU KARANTA: Gwamnati ta na tafka asarar miliyoyin bayan rufe wasu iyakoki

3. Hukumar NIGCOMSAT

Hukumar NIGCOMSAT mai kula da faifen satalait na Najeriya na da aikin gyara karfin na’urarta domin hasko fadin kasar da kyau kamar yadda sabon Ministan kasar ya gindaya mata a jiya.

4. Hukumar NITDA

Isa Pantami ya nemi magajinsa a NITDA ya dage wajen ganin an samu karuwar masu amfani da na’urorin gafaka da manhajojin gida a ma’aikatu. Ana kuma so ma’aikatu su rika amfani da na’urorin zamani wajen aikinsu.

5. Hukumar NIPOST

Sabon Ministan sadarwa ya nemi NIPOST ta kara kokari wajen aika sakonni da wasiku a fadin kasar. Isa Ali Pantami ya kuma bada umarni ga hukumar ta kara yawon wuraren da ta ke shiga.

6. Hukumar USPF

A karshe mai girma Ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami bai bar ma’aikatar USPF da ke karkashinsa a baya ba, inda ya nemi ta rage tazarar da ake samu wajen aiki tsakanin Birane da karkara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel