A wannan masallacin da ka rushe na ke sallah tare da Iyalina – Asari ya fadawa Wike

A wannan masallacin da ka rushe na ke sallah tare da Iyalina – Asari ya fadawa Wike

Shugaban kungiyar nan ta Niger Delta People’s Volunteer Force, Asari Dokubo, ya karyata gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a game da maganar ruguza wani masallaci a cikin jihar.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, Asari Dokubo, ya bayyana cewa babu shakka Nyesom Wike ya rusa wannan babban masallaci na Trans-Amadi da ake magana da ke cikin Garin Fatakwal.

Gwamnatin Nyesom Wike ta na ikirarin cewa ba ta ruguza wani masallaci ba, amma a wani bidiyo da ke yawo a kafafen zamani, Asari Dokubo ya musanya abin da gwamnan ya fada, yana cewa:

“Ina cikin masu yin sallar jam’i a babban masallacin na Trans Amadi. A nan na ke sallah da iyalina.”

“Ni kadai, ina da ‘Ya ‘ya 21, kuma ina zama ne tare da yara 59 na sauran mutane. Mafi yawansu, su na sallah.”

KU KARANTA: Malami ya fito ya yi tir da cin kashin da ake yi wa 'Yan Arewa a Kudancin Najeriya

“Wike ya na ikirarin cewa babu masallaci, karya ce. Karya yake yi kuma kun sani. Idan babu masallaci, me ya kai ka wurin? Mun saye filin wannan masallaci daga hannun Dr. Sotonye Amadi.”

“Kiristoci su na sayen fili su gina cocinsu, me ya hana ka rusa cocin na su?”

“Meyasa kai da Takwaranka, Rotimi Amaechi, ku ka ware masallacinmu, ku ka rusa, domin ku hana yin gini. Wanda ya saye fiilin masallacin mutumin Okrika ne ‘Dan kabilar Ijaw.”

“An saye wannan fili ne daga wajen Cif Dr Edward Sotonye Amadi.”

“Meyasa wannan masallaci ya tsone maku ido? Na fada maku cewa wanda ya fanshi wannan fili wani Musulmin Okrika ne, Alhaji Ali Ibiorika. Ina cikin masu bin sallah a nan.”

Dokubo ya yi watsi da maganar da gwamnan ya yi na cewa Ribas ta kiristoci ce, ya ce Musulmai su na zaune ba su kashe ‘dan kowa ba, ya kara da cewa addinin Musulunci ya fi karfin gwamnan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel