Wani mutum ya auri wasu 'yammata biyu aminan juna a lokaci guda (Bidiyo)

Wani mutum ya auri wasu 'yammata biyu aminan juna a lokaci guda (Bidiyo)

Wani mutum dan asalin kasar Indonesia ya auri wasu 'yammata aminan juna tare da bayyana cewa ba ya son ya bata wa kowaccensu rai.

Wata kafar yada a kasar Indonesia, 'Vice', ya bayyana cewa batun auren mutumin ga aminan juna ya haifar da cece-kuce a wurin ma'abota amfani da dandalin sada zumunta.

A cikin faifan bidiyon da ke yawo a yanar gizo, an ga 'yammatan biyu biyu a zaune a gefen angonsu yayin da ake daura musu aure.

Faifan bidiyon ya nuna cewa an daura auren mutumin da 'yammatan ne a garin Airtarap da ke yankin Kalimantan.

Kafar yada labarai ta 'Vice' ta bayyana cewa mutumin ya biya makudan kudi ga dangin 'yammatan a matsayin sadakinsu.

DUBA WANNAN: Hotunan kafin aure na wani sojan Najeriya sun narkar zukatan jama'a (Hotuna)

Auren mace fiye da daya ba wata sabuwa ko bakuwar al'ada ba ce a kasar Indonesia, saboda mafi yawan jama'ar kasar na bin tafarkin addinin Islama ne.

Biyan kudi masu yawa a matsayin sadaki a kasar Indonesia wata alama ce da ke nuna cewa miji zai kula da matarsa sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel