Iko sai Allah: Yayin da likitoci suka gama yi mata karyar tagwaye zata haifa, sai gashi ta haifo jarirai biyar a lokaci daya

Iko sai Allah: Yayin da likitoci suka gama yi mata karyar tagwaye zata haifa, sai gashi ta haifo jarirai biyar a lokaci daya

- Wata mata mai shekaru 37 ta haifi jarirai guda biyar a lokaci daya

- Matar dai ta bayyana cewa duk lokacin da ta ziyarci likita suna sanar da ita cewa tana dauke da jarirai biyu ne

- Sai dai kuma wani abu da ya bata mamaki shine yadda ta haifi jariria guda biyar duka a rana daya

Wata mata 'yar kasar Uganda mai suna Sofiat Mutesi ta haifi jarirai guda biyu, abin mamaki kuma daga baya kuma ta kara haifo jarirai mata guda uku duka a rana daya.

Kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito, Sofiat har ta gama nakuda ta dauka cewa 'yan biyu (tagwaye) zata haifa.

A ranar Asabar dinnan 24 ga watan Agusta, matar wacce tayi nakuda ta haifi yaro daya a gida, inda daga baya aka garzaya da ita asibiti a yayin da 'yan uwanta suka gano cewa akwai wani jaririn yana zuwa.

A lokacin da aka isa Sofiat cikin asibiti, jaririnta na biyu an haifeshi inda yazo da girman 1.5kg. Ba a wani dauki lokacin mai tsawo ba sai gashi Sofiat ta kara haifo wasu jarirai guda uku.

KU KARANTA: Bidiyo: Masu garkuwa da mutane sun cafke Jaruma Maryam KK, amma daga bisani tasha dakyar

"Ta haihu cikin koshin lafiya, kuma duka jariran guda biyar lafiyarsu lau, ba kuma tare da wani nakasu ba. Bayan kowacce sa'a uku ana shayar dasu. Mahaifiyar lafiyarta lau, an samu an tsayar da jinin da take zubarwa," in ji wata ungozoma mai suna Maureen Babine.

A cewar mai jegon kowanne lokaci ta ziyarci likita suna fada mata cewa tana dauke da jarirai biyu ne.

"Nayi mamaki matuka da naga na haifi jarirai biyar saboda lokacin dana je gwaji , likita ya bayyana mini cewa ina dauke da jarirai biyu ne a cikina," in ji mai jegon.

Yanzu haka dai mai jegon tana ta faman samun 'yan barka da suke taimaka mata da kayan barka da kudi wanda za ta samu ta hada domin rainon jariran nata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel