Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduna (Hotuna)

Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduna (Hotuna)

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, ta karbi bakuncin yaron nan dan baiwa, Joshua Beckford, wanda ya ziyarci Najeriya.

Ya ziyarci jihar Kaduna ne domin yin aiki tare da BMAN domin gina makarantar Sakandire a garin Tafan da ke karamar hukumar Kaura a jihar.

Joshua wani yaro ne mai shekaru 14 da Allah ya yi wa baiwar kaifin basira da matukar kokari, lamarin da yasa har wani take ake yi masa da harshen Turanci 'neuroatypical'

Yana da baiwa a bangarori guda takwas da suka hada da; Lissafi, Yarukan Duniya, Tarihi, Falsafanci, Fasahar zamani, Wasanni, Kimiyya da ilimin 'Art'.

Tun Joshua yana da wata 10 a duniya aka fara koya masa karatu. Ya koyi karatu ba tare da wata gargada a lokacin da ya cika shekaru 2. Ya koyi yaren Japan yana da shekaru biyu da rabi, kuma a lokacin ya fara koyon yaren China, Mandarin.

Joshu ya kammala wani karatu na musamman a kan karatun Falsafanci da Tarihi a jami'ar Oxford da ke kasar Ingila. Ya fita da sakamako mafi daraja (Distinction).

Ya samu wata lambar yabo bayan ya samar da amsar wasu tambayoyin lissafi guda 29,000 a wata gasa da ake yi a yanar gizo.

Yanzu haka Joshua, mai shekaru 14, ya kammala karatunsa na digiri.

Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduba (Hotuna)
Joshua Beckford a jihar Kaduna
Asali: Facebook

Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduba (Hotuna)
Joshua Beckford a gidan gwamnatin Kaduba
Asali: Facebook

Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduba (Hotuna)
Joshua Beckford ya isa jihar Kaduba
Asali: Facebook

Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduba (Hotuna)
Joshua Beckford da Hadiza Balarabe
Asali: Facebook

Bawan Turawan Ingila: Joshua Beckford, yaro dan baiwa ya isa jihar Kaduba (Hotuna)
Joshua Beckford a fadar gwamnatin jihar Kaduna
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel