Ya dace Tinubu ya ci gajiyar Buhari a 2023 - Razaq

Ya dace Tinubu ya ci gajiyar Buhari a 2023 - Razaq

A yayin da ake ci gaba da mayar da yawu da tafka muhawara a kan babban zaben kasa na 2023, wani jigo na jam'iyyar APC, Lanre Razaq, ya bayyana ra'ayi da kuma muradi don ganin tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu ya karbi ragamar jagorancin kasar.

Mista Lanre ya ce kanwa uwar gami na jam'iyyar APC wato Tinubu, ya mallaki duk wata cancanta dai zai iya rike akalar mulkin kasar nan cikin aminci.

A yayin ba da tabbacin cewa babu wani dan siyasa da ya sha gaban Tinubu ta fuskar cancantar jan ragamar kasar nan, babban jigon na APC cikin yakini gami da kyautata zato, ya ce Tinubu zai iya kwantanta kwazon da yayi a bisa kujerar gwamnatin jihar Legas wajen riko da akalar jagorancin kasar nan baki daya.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, furucin Mista Lanre ya zo ne a cikin wata sanarwa da ya gabatar yayin ganawa da manema labarai na jaridar New Telegraph a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta.

KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2020: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na farko a wa'adin gwamnatin Buhari na biyu

A cewar Mista Lanre, magadan kujerar gwamnatin jihar Legas na ci gaba da riskar bagas da rahusa ta karkatar da akalar jagorancin jihar a sanadiyar managarcin tubali da Tinubu ya assasa yayin jagorancin jihar a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya musanta rade-radin kasancewarsa jagoran yi wa Tinubu yakin neman zabe a Arewa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel