A addini, mukami ba abin taya murna ba ne Inji Sheikh Isa Pantami

A addini, mukami ba abin taya murna ba ne Inji Sheikh Isa Pantami

A cikin kwanakin nan ne aka shirya wata walima ta musamman domin taya Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami murnar zama Minista. Sabon Ministan ya fashe da kuka yayin da ya ke jawabi a wurin.

Sabon Ministan ya bayyana cewa shugabancin abu ne na nauyin al’umma da kuma jarrabawa da musiba ga wanda a ka ba. A daidai wannan gaba ne Ministan ya fashe da kuka saboda ganin alhakin wuyansa.

Babban Malamin addinin Musuluncin kuma masanin aikin Boko ya fara da cewa a addinance babu wani dalili na yi wa wanda ya samu mukami ko karin matsayi, ko kuma a ka zabe shi a wata kujera murna.

A cewar Isa Ali Pantami, tun da alhaki ne a kan mutum na jagorantar al’umma ko kuma shugabantar su ko wakilci, ba wanda ya samu wannan matsayi za a yabawa ba, sai dai mutanen da ke kasansa.

Yayin da ya ke jawabinsa a cikin harshen Ingilishi, Sheikh Isa Pantami ya nuna cewa mutane ya kamata a rika tayawa da farin ciki idan har wani mutumin kwarai ya samu kujerar shugabanci ba mutumin ba.

KU KARANTA: Shin wanene sabon Ministan Tarayya Isa Ali Ibrahim Pantami

Ministan tarayyar ya ke cewa jama’an Najeriya ya je yi wa aiki ba karan kan sa ba. Dr. Pantami ya yi wannan jawabi ne a wurin walimar da Abokan ibadansa na masallacin Annur su ka shirya a birnin Abuja.

A wannan bidiyo da wani mai suna Ismail Ilah ya buga a shafin Tuwita, za a ga Ministan ya hakura da jawabi bayan kuka ya zo masa. Za a ji inda wasu su, su ka nemi a mika masa tsummar share fuska.

Haka zalika wannan shi ne ra’ayin wanda ya gaji Isa Pantami a kujerar hukumar NITDA watau Kashifu Inuwa wanda ya ce taya shi murna tamkar taya Likitan da zai yi fida murna ne kafin ya shiga aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel