Fasa-ƙauri: 'Yan gudun hijira 33, motoci 15, da buhunan Shinkafa sun fada hannun Kwastam

Fasa-ƙauri: 'Yan gudun hijira 33, motoci 15, da buhunan Shinkafa sun fada hannun Kwastam

Jami’an hukumar Kwastam na Najeriya masu maganin fasa kauri sun cafke wasu mutane 33 da su ka yi kokarin shigowa cikin kasar a boye. Kakakin hukumar ya sanar da wannan a makon nan.

A Ranar Talata, 27 ga Watan Agusta, 2019, Mai magana da yawun bakin hukumar ta Kwastam, Joseph Attah, ya bayyana cewa su na samun nasara a shirin nan na “Exercise Swift Response.”

Mai magana a madadin hukumar, ya ce hakar wannan aiki ta na cin ma ruwa domin sun kama masu shigowa Najeriya babu takardu, sannan kuma sun tare wasu motoci da kayan fasa kauri.

Motoci 33 da aka shigo da su Najeriya ta barauniyar hanya su ka kare a hannun jami’an na NCS. Daga cikin kayan da aka samu har da buhuna 3560 na shinkafar kasar waje masu nauyin kilo 50.

KU KARANTA: Za a yi wa wasu manyan Jami'an Kwastam fiye da 300 ritaya

Bayan haka kuma jami’an kasar sun cafke wasu buhuna takin zamani na NPK 59 da aka nemi a shigo da su a boye. A jawabin da Attah ya fitar jiya, ya ce sun kuma kama masu shigo da mai.

Gangar man gyada 65 jami’an na Kwastam su ka karbe a wajen wannan aiki da a ke yi na “Exercise Swift Response.” Ma’aikatan sun kuma dakile manyan ganguna 12 dauke da fetur.

Ofishin NSA mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Najeriya ne ya kawo wannan aiki na “Exercise Swift Response.” Kwastam ta na aiki ne da sauran hukumomi irinsu ‘yan sanda.

Yanzu dai an fara ganin tasirin wannan aiki na hadaka da a ke yi da jagorancin kwastam da NIS masu kula da shiga da fice da kuma Dakarun sojin sama da sauran jami'ai a yankunan kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng