Yan Sanda sun aikawa Aminu Ladan (ALA) sammaci a Jihar Kano

Yan Sanda sun aikawa Aminu Ladan (ALA) sammaci a Jihar Kano

Mun samu labari cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen Kano sun aikawa shararren Mawakin nan na Hausa, Aminu Ladan Abubakar wanda aka fi sani da ALAN Waka sammaci.

‘Yan Sandan na jihar Kano sun aikawa sun aika takarda ne ga ALAN Waka a Ranar Litinin 26 ga Watan Agusta, 2019. An nemi Mawakin ya bayyana gaban jami’an kasar a mako mai zuwa.

Takardar ta nuna cewa jami’an tsaron su na wani bincike ne da ya shafi Mawakin. A wannan takarda da ta shigo hannun Legit Hausa, ba a bayyana ainihin bincike ko zargin da ke kan Alan ba.

‘Yan Sandan sun tura takardar ne ga dakin wakansa da ke kan titin gidan Zoo a cikin Unguwar Hausawa da ke Garin Kano. Ba mu da labarin ko babban Mawakin ya fito ya yi magana kawo yanzu.

An nemi babban Mawakin ya mika kansa ne a Ranar Litinin, 2 ga Satumba, 2019 da karfe 10 na safe a gaban jami’in da ke kula da harkokin siyasa a babban Hedikwatar Rundunar ‘yan sanda na Kano.

KU KARANTA: Tsohon yaron Jonathan ya caccaki Gwamnan Kano Ganduje

Yan Sanda sun aikawa Aminu Ladan (ALA) sammaci a Jihar Kano
Takarda zuwa ga Aminu Ladan Abubakar da ta fito Ranar Litinin
Asali: Twitter

Takardar ta fito ne daga sashen CID masu kula da sha’anin binciken manyan laifi. Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Paul Odama shi ne ya sa hannu a wannan takarda a madadin Kwamishina.

Malam Aminu Ladan Abubakar (Alan waka) ya kan yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wakokin siyasa, sai dai ya na cikin wadanda su ka yi wakokin adawa ga gwamnatin APC ta jihar Kano.

Ba wannan ba ne karon farko da ALA zai shiga hannun 'yan sanda a Najeriya. A shekarun baya, har sai da a ka rufe Mawakin na wani lokaci inda bayan ya fito ya bada labarinsa a cikin wata waka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel