Kwamred Shehu Sani ya ci kasuwar Ranar Hausa a shafinsa na Tuwita

Kwamred Shehu Sani ya ci kasuwar Ranar Hausa a shafinsa na Tuwita

A jiya ne a ka yi bikin harshen Hausa a Duniyar kafafen sadarwa na zamani da yada labarai. Shekaru kusan hudu kenan yanzu a duk shekara a kan yi bikin #RanarHausa a watan Agusta.

An ware Ranar 26 ga Watan Agustan kowace shekara ne domin tunawa da harshen Hausa. Masu jin wannan yare da kuma wanda su ka iya shi su kan fito domin yin bajakolin fasahar su a ranar.

Wannan karo ba a bar tsohon Sanatan nan na jihar Kaduna watau Shehu Sani a baya ba, inda ‘dan siyasar ya yi amfani da shafinsa na Tuwita ya rika aman wasu karin maganganu masu ban kaye.

Wadanda ke bin tsohon ‘dan majalisar a shafin na sa sun yaba da irin salon harshen sa tare da yayata wadannan karin maganganu da ya rika shararawa domin cin kasuwar wannan rana.

KU KARANTA: Wani sabon tsarin karbar haraji ya sa an yi ca a kan shugaba Buhari

Daga cikin karin magaganun da Sanatan da ya wakilci Birnin Kaduna ya kawo akwai; “Gyangyadi ya kare, aska ta iso wuya.” Ya kuma rubuta “Saurayi ba kwabo, gwangwala da suffan rake.”

A wasu lokutan ya rubuta: “Maza ba mata bane, dan daudu ya karya sabulu.” da irin su “Samun Wuri, 'Dan cirani da barcin rana.” da kuma irinsu: “Tsoho da kudi, dumamen tuwon shinkafa.”

An kuma ji Sanatan ya na cewa “Shegiya duniya, tsoho ya tauna kashi.” Wannan ya jawo surutu har wasu su ka rika tura masa wani hoton shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na sakace baki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel