Gwamnatin Legas ta shirya wani babban taro ba ta aikawa Ambode goron gayyata ba

Gwamnatin Legas ta shirya wani babban taro ba ta aikawa Ambode goron gayyata ba

A cikin ‘yan kwanakin nan ne gwamnatin jihar Legas karkashin Mai girma Babajide Sanwo-Olu ta shirya wani taron bita ga manyan jami’an ta. A karshen makon nan ne a ka gama wannan taro.

Sababbin Kwamishinonin jihar Legas da manyan Sakatarori na din-din-din na jihar sun halarci wannan taro da a ka yi na tsawon kwanaki hudu. An gayyaci manyan jihar Legas wajen wannan taro.

Kamar yadda mu ka samu labari, Jide Sanwo-Olu ya gayyaci tsofaffin gwamnonin Legas na APC da su ka shude domin su yi bayani a wajen taron bitar. Amma da alamu ba a gayyaci Akinwumi Ambode ba.

An samu ganin tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Magajinsa Babatunde Fashola a otel din. Amma an nemi Akinwumi Ambode wanda ya bar mulki kwanan nan an rasa.

Da ‘yan jaridar Premium Times su ka yi kokarin tuntubar tsohon gwamnan sai ya nuna cewa babu wanda ya gayyace sa. Habib Aruna wanda ke magana a madadin Akinwumi Ambode ya bayyana wannan.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya jinjinawa Akinwumi Ambode

Mista Habib Aruna ya fadawa Manema labarai ta wayar salula cewa: “Ku tambaye su abin da ya hana su gayyatar Ambode. Aruna ya cigaba: “Su ne za fi sanin abin da ya hana su kiran shi wajen taron.”

Rahotanni sun ce da ‘yan jarida su ka yi kokarin samun gwamna mai-ci a waya, ba a dace ba. An samu wayar mai magana da yawun bakin Sanwo-Olu a kashe a Ranar Lahadi, 25 ga Watan Agusta.

Bola Tinubu da Raji Fashola sun yi magana a wajen wannan bita da a ka gudanar. Shi kuma Gwamna Babajide Sanwo-Olu yanzu haka ya na kasar waje tare da shugaban kasa Buhari wajen wani taro.

Akinwumi Ambode ya sha kasa a yunkurin sake komawa gidan gwamnatin jihar Legas bayan da ya rasa tikitin jam’iyyar APC a hannun gwamna mai-ci. Yanzu ma haka hukumar EFCC ta soma bincikensa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel