To fah: Zamu yi tankade da rairaya a hukumar 'yan sandan Najeriya - Shugaba Buhari

To fah: Zamu yi tankade da rairaya a hukumar 'yan sandan Najeriya - Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi Sarakunan gargajiya na arewa a fadar shi

- Sun tattauna ne akan yanda za'a kawo karshen rashin tsaro dake addabar al'umma

- Shugaban yace Sarakunan gargajiya ne suka fi kusa da al'umma don haka sunfi sanin kalubalen da ake fuskanta

Yau Juma'a Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa zata kawo gyare-gyare da canje-canje a hukumar 'yan sanda kasa.

Buhari ya sanar da hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Sarakunan gargajiya na arewacin Najeriya.

Ya lissafo kadan daga cikin kokarinsa na gyara da canji ga gyaran aiyukan hukumar wandan suka hada da, daukar karin ma'aikata da kuma isasshiyar horarwa.

A yau din ne Shugaba Muhammadu Buhari, a Abuja yace an gyara tsarin hukumar 'yan sandan tare da samar musu da sabbin kayan aiki domin shawo kan kalubale a fadin kasar nan.

Shugaba Buhari yace, dawo da ma'aikatar kula da harkokin 'yan sanda anyi ta ne don tabbatar da sabbin tsarin na samar da tsaro ga rayuka da kadarorin jama'a, hadi da kashe hanyoyin yaduwar ta'addanci.

"Na yanke shawarar haduwa da masu martaba ne don tabbatar muku da cewa a shirye gwamnati take da ta shawo kan duk matsalolin tsaro dake addabar kasar nan.

" Wannan haduwa ce don saka sarakunanmu tsundum, ta yadda zamu hada karfi wajen shawo kan matsalolin tsaro dake addabar kasar nan.

"Ya zama dole a garemu, da mu taka rawar gani wajen shawo kan matsalar. Ballantana masu sarautar gargajiya, saboda kunfi kusanci ga al'umma," inji shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hori sarakan dasu goyawa jami'an cibiyoyin tsaro baya ta hanyar basu bayanai gamsassu na mutanen da suke mulka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel