Ambaliyar ruwa ta ci gidaje a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa

Ambaliyar ruwa ta ci gidaje a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, ambaliyar ruwa da ta auku a sanadiyar ci gaba da saukar ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ta lalata hanyoyn Guri-Adyani da Guri-Dolanzugo a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Wata sanarwa da kakakin karamar hukumar Guri, Alhaji Sanusi Doro ya fitar ta bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta jefa manoma masu fidda amfanin gona kamar su shinkafa, ridi, kankana da albasa, cikin tsaka mai wuya a sanadiyar rashin samun hanyar zuwa kasuwanni.

A sanarwar da Alhaji Doro ya fitar cikin garin Guri a ranar Asabar, ya ce aukuwar ambaliyar ruwan ta yiwa al'ummomin Dolanguzo da Adyani daurin dabaibayi inda ta haramta masu shige da fice.

Kazalika dai sanarwar ta bayyana cewa, a yayin da ambaliyar ruwan ta ci gidaje 400, mazauna garin Guri sun kauracewa muhallansu inda suka nemi mafaka a wasu makarantu na yankin.

Kara karanta wannan

Rudani: Jamhuriyar Nijar ta musanta samun tallafin motocin miliyoyi da Buhari

Ya ce "ambaliyar ruwan ta raba daruruwan mutane da muhallansu inda suka nemi mafaka a wasu manyan makarantun sakandire biyu na Arabiya dake garin Guri".

KARANTA KUMA: Harin Ekweremadu: A sanar da mu idan manyan Najeriya za su kawo ziyara - Gwamnatin Jamus

Babban jami'in karamar hukumar ya ce, ya zuwa yanzu garuruwan da ke fuskantar barazanar ambaliya sun hadar da Musari, Gaduwa, Abunabo, Zoriyo, Margadu da kuma Dagana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangane da yunkurin magance radadi tare da bayar da agaji, Alhaji Doro ya yabawa gwamnatin jihar da ta bayar da tallafin barguna, gidajen sauro da kuma kayan abinci ga wadanda annobar ambaliyar ruwa ta sa suka kauracewa muhallansu.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, Injiniya Mustapha Maihaja, ya ce jihohi 30 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, da cewar mafi akasarin jihohin na kusanci ne da tekun Neja da na Binuwai.

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel