Harkar ilmi: Buhari zai sa albarka a katafaren ginin da CBN ta yi a Jami’ar ABU

Harkar ilmi: Buhari zai sa albarka a katafaren ginin da CBN ta yi a Jami’ar ABU

A cikin ziyarar aikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo jihar Kaduna, zai zo har jami’ar Ahmadu Bello inda zai kaddamar da wani katafaren gini da babban bankin Najeriya ta gina.

Shugaba Buhari ne zai bude wannan gine-gine da babban bankin CBN su ka yi a cibiyar cigaba da karatu na babbar jami’ar tarayyar da ke cikin Samaru a Garin Zariya. Bankin na CBN ya bayyana wannan.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, a Ranar Alhamis 22 ga Watan Agustan 2019 ne shugaban kasar zai tofawa wannan wuri da a ka gina albarka. A farkon 2019 an bude irin wannan gini a Enugu.

An gina wannan wuri ne domin karatun abin da ya shafi ilmin harkar kasuwanci da kudi a wannan jami’a ta ABU Zaria. Isaac Okorafor, a madadin CBN ya ce an yi wannan ne domin bunkasa tattali.

KU KARANTA: An fara kafa Gwamnati a Najeriya; Buhari ya rantsar da SGF

Harkar ilmi: Buhari zai sa albarka a katafaren ginin da CBN ta yi a Jami’ar ABU
Ginin "center of excellence" da a ka gina a cikin Jami’ar ABU
Asali: Twitter

CBN ta ke cewa: “Ginin Zariya ya na kunshe da dakin taro mai daukar mutane 360, da kuma dakunan daukar darasi da zai iya cin mutum 544. Akwai kuma karamin dakin karatu mai kujeru 240.”

Duk a cikin wannan gini za su samu dakin lacca mai dauke da na’urorin jawabi na zamani da kuma wurin dafa abinci da dakin gafaka mai cin mutum 50. Akwai kuma wurin karatun mutane 68. Inji CBN.

Ba a nan kurum wannan katafaren gini ya tsaya ba domin kuwa an shimfida ofisoshin ma’aikata da kuma wurin kwanan yaran makaranta gangariya har da dakin yin atisaye ga masu bukatar motsa jiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel