The Millions: Sabon fim din su Ali Nuhu zai fito a karshen Agusta

The Millions: Sabon fim din su Ali Nuhu zai fito a karshen Agusta

Fitaccen ‘dan wasan kwaikwayon Hausa, Ali Nuhu, ya yi wani fim na Ingilishi a Najeriya tare da manyan ‘yan wasa irin su Ramsey Noah. A karshen watan Agustan nan za a fara fito da wannan fim.

Kamar yadda mu ka samu labari, an tara manyan ‘yan wasan Nollywood a cikin wannan babban shiri mai suna “The Millions”. A Ranar Juma’a 30 ga Watan Agusta za a haska wannan fim a gidajen kallo.

Chika Lann ce ta shirya wannan fim yayin da Toka McBaror da kuma Tunde Apalowo su ka bada umarnin shirin. Tun a farkon shekarar nan dinbin mutane su ka fara jiran a kammala wannan fim domin su kalla.

Sauran manyan ‘yan wasan da su ka fito cikin wannan shiri sun hada: Toyin Abraham, Blossom Chukwujekwu, Nancy Isime, ita kan ta Mai shiryawa Chika Lann, da kuma irin su Etinosa Idemudia.

KU KARANTA: Wata Jarumar Indiya ta wulakanta Ali Nuhu a Instagram

Har wa yau fitaccen mai wasan barkwancin nan a Najeriya da kasashen waje watau Ayo Makun wanda a ka fi sani da AY Comedian ya na cikin shirin, Broda Shaggi da Agbero duk sun fito a wannan wasa.

A wannan fim din da a ka yi a manyan Biranen Kaduna da Abuja, za a ga Ramsey Nouah, AY Comedian da Blossom Chukwujekwu sun tafi fashi da makami. Jama’a za su so su ji ya za a kare wannan shiri.

Ali Nuhu ya na cikin manyan Taurarin wasan kwaikwayon Hausa wanda ya yi shekara da shekaru ya na fina-finai. Ali Nuhu ya kan kuma yi fim da Ingilishi a masana'antar Nollywood.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel