PDP: INEC ta karawa El-Rufai kuri’un haram a zaben Kaduna

PDP: INEC ta karawa El-Rufai kuri’un haram a zaben Kaduna

Mun samu labari cewa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da ‘dan takararta na gwamna a jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan sun damfari kotu domin a rusa wasu kuri’u a zaben da ya gabata.

Jam’iyyar PDP da Isah Ashiru Kudan su na rokon Alkalan da ke sauraron korafin zaben gwamna da aka yi a jihar Kaduna da su soke kuri’u 515, 951 da su ke ikirarin cewa bai kamata a tattara da su ba.

A jiya, 20 ga Watan Agusta, 2019, kotu ta sa rana domin ta saurari batun karshe a shari’ar. A jawabin da jam’iyyar PDP mai korafi za ta gabatar a karshe, PDP za ta bukaci a rusa wadannan kuri’u.

Lauyoyin jam’iyyar hamayyar su na neman Alkalai su gabatar da Isa Ashiru Kudan a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Kaduna a dalilin cewa shi ne wanda ya tashi da mafi yawan kuri’u a doka.

PDP ta iya gabatar da shaidu 135 daga cikin 685 da ta tara daga zaben inda su ka tabbatarwa kotun da ke sauraron korafin zabe cewa an tafka magudi da satar akwati da laifuffuka iri-iri a Kaduna.

KU KARANTA: Kano: INEC ta fara kare kan-ta a shari'ar Ganduje da Abba

Rt. Ashiru Kudan ya fadawa kotu cewa hukumar zabe na INEC ta karawa Abokin takararsa na APC watau gwamna Nasiru El-Rufai kuri’u 391, 741 tare da lafta masa wasu kuri’u 124, 210 ta bayan fage.

Masu kare PDP da ‘dan takarar ta a kotu sun ce bayyana Nasir El-Rufai da INEC ta yi a matsayin wanda ya ci zabe ya sabawa doka. Lauyoyin sun nemi a cire kuri’u 391,741 daga abin da APC ta samu.

Haka zalika Lauyoyin Isa Kudan sun bukaci a rage kuri’a 124,210 daga kuri’un ‘dan takararta. A cewar Lauyoyin wannan ne ya dace da doka. Idan a ka yi haka PDP za ta lashe zaben da kuri’u 36, 272.

Daily Trust ta rahoto cewa manyan Lauyoyin PDP a shari’ar sun hada da Emmanuel C. Ukala SAN, Donald Denwigwe SAN, Cif Ferdinand O. Orbih SAN, Elisha Y. Kurah SAN da kuma wasu Lauyoyi har 14.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel