Umurnin kwace kadarorin Najeriya a Birtaniya: Gwamnatin Buhari na shirin kama wasu jami’ai da ke da hannu a hukuncin

Umurnin kwace kadarorin Najeriya a Birtaniya: Gwamnatin Buhari na shirin kama wasu jami’ai da ke da hannu a hukuncin

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ce tana duba yiwuwar kama wasu jami'ai da ta ke zargi da hannu a wani hukunci da kotun kasar Birtaniya ta yanke, inda ta bukaci sai ta biya wani kamfani tsabar kudi har dala biliyan 9, saboda saba yarjejeniya da suka kulla.

Wata kotun Landan ce ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya kamfanin Process & Industrial Developments Ltd (P&ID) wadannan makudan kudade ta hanyar kwace kadarorinta, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ce lamarin tsohuwar shari'ah ce da jami'an gwamnatocin da suka gabata suka gaza wajen daukaka kara, har damar ta rufe.

"Masu mulki a wancan lokacin ba su daukaka kara ba har kofa ta rufe," in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin Buhari ta yi kokarin ganin matakin da za ta dauka domin jinkirta aiwatar da hukuncin domin bude kofar ta daukaka kara amma kotun a Ingila ta ce ba zata bayar da wannan dama ba.

Ya zargi jami'an gwamnatin baya da yin sakaci kan abin da ya kira hadin bakinsu don a cuci Najeriya har suka bari abu ya kasance haka.

Ya ce duk da gwamnati za ta daukaka kara amma abu na farko da za a yi shi ne duk wani wanda aka san da hannunsa a cikin wannan hadin baki don a cuci Najeriya tare da wani kamfani na kasar waje, gwamnati za ta sa a kamo su kuma za ta dauki mataki akansu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gobara ta tashi a sananiyyar kasuwar Katangowa da ke Lagas (hotuna)

A wani labari na dabam, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Fadar Shugaban kasa a ranar Lahadai, 18 ga watan Agusta, ta yi Karin haske cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai haramta ko sanya takunkumi akan shigo da abinci kasar ba.

A wani jawabi daga babban hadimin Shugaban kasa akan harkokin labarai, Mallam Garba Shehu, ya ga laifin fassarar da rahoton financial Times ya yi akan lamarin.

Shehu yace babu wani haramci ko takunkumi da aka sanya kan shigo da abinci, inda ya kara da cewa har anzu masu shigo da kayayyakin abinci na da damar neman chanjin kudinsu daga hukumomi masu zaman kansu domin cimma harkokinsu na shigo da kayayyakin abincin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel