Jihohi 10 da dalibai suka fi cin jarrabawar WAEC a 2019

Jihohi 10 da dalibai suka fi cin jarrabawar WAEC a 2019

Jihohin Abia, Anambra da Edo na sahun gaba a cikin jerin jihohin da dalibansu suka yi kwazo a bangaren cin jarrabawar kammala makarantar sakandire da hukumar tsara jarrabawar kammala karatun sakandire a nahiyar Afrika ta yamma (WAEC) ta tsara.

A wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa, ta ce hukumar WAEC ta fitar da wata dala da ke nuna kokarin kowacce jiha a sakamakon jarrabawar da ta fitar kwanan nan.

A yayin da jihohin Abia, Anambara da Edo ke sahun farko a cikin jerin jihohin da dalibansu suka yi kokari a sakamakon jarrabawar, jihohin Jigawa, Zamfa da Yobe na can sahun baya karshe a cikin jerin jihohin.

A cewar mizanin auna kwazon daliban, jihar Legas ce kadai ta shiga sahun jihohi 10 na farko daga jihohin yankin kudu maso yamma na 'yan kabilar Yoruba.

Kaduna ce jihar Arewa da daliban ta suka fi nuna kwazo a jarrabawar, amma kuma ita ce jiha ta 12 a a mizanin auna kwazon jihohin Najeriya.

DUBA WANNAN: Waiwaye: Yadda aka kori Zakzaky daga jami'ar ABU saboda haddasa rikici a shekarar 1979

Duk da aiyukan 'yan bindiiga da suka addabi jihar Zamfara, ta zo a mataki na 36, inda ta dara jihar Yobe, wacce ke mataki na 37.

Jihohi 10 da ke sahun farko a mizanin auna kwazon dalibai ta fuskar cin jarrabawar WAEC su ne; Abia, Anambra, Edo, Ribas, Imo, Lagos, Bayelsa, Delta, Enugu da Ebonyi.

While Adamawa, Osun, Sokoto, Bauchi, Kebbi, Katsina, Gombe, Jigawa, Zamfara, and Yobe occupy the bottom 10 of the chart.

A yayin da jihohin Adamwa, Osun, Sokoto, Kebbi, Katsina, Gombe, Jigawa, Zamfara da Yobe suka kasance jihohi 10 da e sahun baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel