Saboda jama’a su tabbatar da jinsi na, na ke yawo a tuɓe – Inji Caster Semanya

Saboda jama’a su tabbatar da jinsi na, na ke yawo a tuɓe – Inji Caster Semanya

Babbar ‘Yar wasan tseren nan ta Duniya, Caster Semenya, ta bada labarin cewa a wasu lokutan ta rika yawo tsirara a dakin ‘yan wasa saboda Abokan tseren ta su tabbatar lallai ita ma Mace ce.

Caster Semenya ta kasar Afrika ta Kudu ta dade a na yi mata zargin cewa Mata-Maza ce, ta bayyana cewa da gan-gan ta kan yi yawo zigidir a daki haihuwar Uwarta domin ta wanke kan ta.

Semanya ta ce za ta iya tunawa ta kan yi tafiya tsirara a dakin ‘yan wasa saboda wasu sa'o'in na ta su gane ainihin jinsin ta. 'Yar wasar ta yi wannan jawabi ne wajen wani taron mata da a ka yi.

Semanya ta ke cewa sauran Abokan hamayyar ta su na bukatar su tabbatar cewa Mace ce irin su domin su samu jin dadin yin tsere da ita. ‘Yar wasar ta ce duk rana ta ka yin tafiyar mil bakwai.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun shiga Kauye cikin tsakar dare sun hallaka mutane

“Mafi yawan lokaci ina atisaye ne a cikin daji. Ba na jin tsoron Magauta domin ina rufe masu baki. Ina cikin ‘yan matan da sam ba su da tsoro. Ina da buri na, na san zan ci ma nasara a rayuwa.”

‘Yar wasan ta cigaba da cewa: “Mahaifi na ya yi mani sha’awar in yi kwallon kafa, amma na ba shi kunya na saida takalman kwallo na. Wannan ya ba shi mamaki, abinci na ya na cikin tsere.”

Yanzu haka an hana Caster Semanya tsere a Duniya muddin ba ta amfani da magungunan da ke rage karfin kwayoyin jinsin halitta. A na zargin cewa jikin ta ya sha banban da sauran mata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel