Shugaba Buhari ya yi magana bayan IBB ya isa shekara 78 a Duniya

Shugaba Buhari ya yi magana bayan IBB ya isa shekara 78 a Duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon Abokin aikinsa kuma shugaban kasa a lokacin mulkin Soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, murnar cika shekara 78 da haihuwa.

Kamar yadda Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya watau Garba Shehu ya bayyana, Buhari a madadin daukacin gwamnatinsa da Iyalinsa da sauran ‘Yan Najeriya su na taya IBB murna.

A jawabin na Malam Garba Shehu, shugaban kasar ya nemi Ibrahim Badamasi Babangida ya karbi gaisuwar sa. Buhari ya jinjinawa irin kokarin da tsohon shugaban kasar ya yi wa Najeriya a rayuwarsa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ke cewa IBB: “A daidai wannan rana ta musamman a rayuwar ka, mu na tunawa da irin namijin kokari da bautar da ka yi a gidan Soja domin tsare martabar Najeriya.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nemi Sojoji su ga bayan masu addabar Jama'a

Buhari ya kara da cewa: “Mu na godiya da irin kishin kasar da ka ke nunawa wajen sha’anin tafiyar da Najeriya. Yayin da ka ke kara shekaru a ban kasa, za mu cigaba da neman shawara da dattakunka”

Ina addu’a ga Ubangiji ya kara maka lafiya da kwarin gwiwa domin taimakawa Iyalinka da kasar nan. Shugaban kasar ya rufe jawabin da ke cikin wasikar ta sa ta 17 ga Watan Agusta da wannan kalamai.

A daidai wannan lokaci, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taya Janar Ibrahim Babangida murnar wannan rana ya na cewa ya gyara fuskar kasar nan da tattalin arziki a lokacinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel