Tsaffin gwamnonin da suka shiga taska mai wuya bayan barin mulki a 2019

Tsaffin gwamnonin da suka shiga taska mai wuya bayan barin mulki a 2019

Babban zaben shekarar 2019 ya zo ya kuma wuce. Kazalika, Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya zabi wanda zai nada a matsayin ministoci. Sai dai yayin da wasu ke cike da farin ciki da murna wasu na nan cikin zafin shan kaye.

Cikin wadanda ke fama da radadin shan kayen sun hada da tsaffin gwamnoni da suka gaza komawa kan mulki karo na biyu da kuma wadanda sun kammala wa'adinsu biyu amma sun sha kaye a zaben kujerar sanata kamar yadda ta ke a al'adan gwamnonin Najeriya.

Ga dai jerin wasu tsaffin gwamnonin da za su cigaba da zaman hakuri a kalla na shekaru hudu nan gaba saboda ba su samu shiga fadar shugaban kasa ba bayan sun rasa kujerunsu na gwamna.

1. Abdulaziz Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya lashe zaben kujerar sanata bayan kammala wa'adinsa biyu a jihar. Sai dai daga baya kotun koli ta soke zaben 'yan takarar jam'iyyar APC a 2019 a Zamfara bayan an gano cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani ba.

Hakan yasa kotu ta kwace nasarar ta mika wa jam'iyyun da suka zo na biyu kuma Yari bai samu kujerar minista a fadar Shugaba Buhari ba.

2. Mohammed Abubakar

Tsohon gwamnan na jihar Bauchi ya sha kaye har sau uku a 2019. Ya sha kaye a zaben farko, ya kuma sha kaye a zaben kece raini sannan daga karshe kuma bai yi nasara ba a kotun zabe.

Ya sha kaye ne hannun Bala Mohammed na jam'iyyar PDP kuma baya cikin wadanda Shugaba Buhari ya zaba domin zama minista.

3. Abdulfatah Ahmed

Kafin babban zaben 2019, tsohon gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah ya fara hangen kujerar sanata da mazabar Kwara South da tun a baya ya samu goyon bayan mai gidansa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Sai dai Saraki ya kwace tikitin takarar sanatan daga hannun Ahmed bayan tsohon gwamnan ya gaza kawo akwatinsa a zaben kece raini da aka gudanar da dan takarar gwamnan da Ahmed ya zaba.

Ko da ya ke Ahmed ya musanta cewa kwace takarar daga hannunsa ba ta da alaka da kayen da jam'iyyarsa ta sha a mazabarsa ta Ekiti/Oke Ero/Isin/Irepodun hakan dai na nufin zai yi wuya a dama da shi cikin shekaru hudu nan gaba.

4. Jibrilla Bindow

Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC shima ya sha kaye hannun Umar Fintiri na jam'iyyar PDP a lokacin da ya yi yunkurin tazarce.

Masu nazarin siyasa sun yi hasashen cewa Bindow ya fadi zabe ne saboda yadda ya yi watsi da mutanen karkara ya mayar da hankalinsa kan yi wa birane ayyuka.

Alamun cewa zai fadi zabe ya fito fara fitowa fili ne bayan wasu jam'iyyun siyasa 10 a jihar da suka yi masa mubaya'a da farko suka canja shawara su ka juya masa baya, sunyi hakan ne saboda wai baya bin shawarwarin da suke bashi.

5. Ibrahim Dankwambo

Bayan ya kammala wa'adinsa biyu a matsayin gwamnan jihar Gombe karkashin jam'iyyar PDP, Dankwambo ya yi takarar sanata amma ya sha kaye a hannun Saidu Alkali na jam'iyyar APC wanda ya lashe zaben kujerar sanatan na mazabar Gombe ta Arewa.

Hakan ya sa Dankwambo ya zama dan kallo a gwamnatin Najeriya duba da cewa baya tare da jam'iyya mai mulki.

Wasu tsaffin gwamnonin da su kayi biyu babu sun hada da; Akinwunmi Ambode na jihar Legas da Abiola Ajimobi na jihar Oyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel