Allah ya sanya alkhairi: Fitacciyar mawakiya Maryam Sangandale za ta amarce

Allah ya sanya alkhairi: Fitacciyar mawakiya Maryam Sangandale za ta amarce

- Fitacciyar mawakiyar arewacin Najeriya Maryam Sangandale za ta yi aure a karshen wannan watan da muke ciki

- Mawakiyar ta wallafa sanarwar hakan ne a shafinta na Facebook, inda ta gayyaci 'yan uwa da abokan arziki

- Maryam dai ta samu lambar yabo kala-kala a bangaren manyan mawaka mata na arewacin Najeriya

Fitacciyar mawakiyar nan ta arewacin Najeriya, wacce har yanzu tauraruwarta ke haskawa, Maryam A Baba, wacce aka fi sani da suna Maryam Sangandale ta gama shiri tsaf don amarcewa da angonta a ranar 28 ga wannan wata na Agusta shekarar 2019.

Mawakiyar ta wallafa sanarwar daurin auren nata ne a shafin sada zumunta na zamani na Facebook, inda ta gayyaci masoyanta, 'yan uwa da abokan arziki dake lungu da sako na kasar nan zuwa wajen daurin auren.

KU KARANTA: Ke duniya: An kama wani yaro dan shekara 15 da ya yiwa iyayensa karyar an sace shi don su bashi rabin miliyan kudin fansa

Maryam A Baba dai mawakiya ce da ta yi suna sosai a arewacin Najeriya, inda take wakoki kala-kala a bangaren fina-finan Hausa, biki, siyasa da dai sauransu.

Maryam ta karbi lambar yabo kala-kala a bangaren zakakuran mawaka mata na arewacin Najeriya. Babbar wakar da tayi wacce ta sanya ta yi suna ita ce 'Sangandale', inda dalilin wakar ne yasa aka canja mata suna zuwa Maryam Sangandale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng